19 Mar 2019
kawarta ce sanadi 1 complete hausa novel

Home kawarta ce sanadi 1 complete hausa novel
Mun samar muku da Android Application din wannan littafin domin saukaka muku karatunsa, mun rarrabashi zuwa babi babi ta yadda za ku iya
karantawa kuna hutawa ba tare da kun manta inda ku ka tsaya ba
domin morewa sabon tsarinmu na saukakawa masu karatu danna download da ke kasa


wannan hoton yana nuna yadda tsarin cikin littafin ya ke a cikin wayar Android

kallli shirin dadin kowa sabon salo da dukkan shirye shiryen arewa 24 a wayarka

danna rubutun da ke kasa ka yi download

https://play.google.com/store/apps/details?id=arewa24.tv
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)


WHATSAPP NO:+2349030159301

[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💜💙❤🖤💚💛
KAWARTACE SANADI
💚💛❤🖤💜💙


®zuwairat(ummu Maryam)


1⃣*Alhamdulillah*

*Am back again by the grace of Allah*

*Please kar Wanda ya chanza min littafi ba tare da izinina ba*

*_Wannan littafin is nothing but a fiction*


*Kuma Dan Allah kar Wanda ya hada min photos na stars kuma in mutum yayi har ga Allah ban yafeba*Wasu mata ne zaune cikin wani katafaren falo, dukkan su sanye suke da Vail banda daya wance take da alaman cikin gidanta take, duk fuskokinsu looks sad, daya daga cikin Matan mai kama da matangidan tace
"Ni har yanzu ban gane wannan abunba...ya zaayi cikin shekara daya maneman auren yarinyan nan su dinga ja da baya?... Kuma duk sai sun kawo lefe amma daga baya su fasa?..." Bata idaba wata ta katseta dacewa
" kema dai kin fada....wannan abun da gani ba haka nan bane...there is something big behind this... Yarinyan nan ba wani mugun hali gareta balle ace kilan bincike suke kanta....nidai gaskiya Hadiza mu mike tsaye.... " tafada tana kallon matan gidan, Ahankali Matan ta cire hannun ta daga tagumin datayi ta kallesu Sannan tace
"Yanzu sis me zanyi?...hmmm...nidai nasan kawai lokacin aurenta ne baiyi ba....besides by daughter is just 20 years old.. Name zan dami kaina?..." Tafada cikin sanyin murya,
"Daman abinda zakice kenan...to let me warn you... Wannan abun dake faruwa is not just like that....this is a bad omen,...ya zaayi yarinya son kowa kin Wanda ya rasa ta zama tamkar abun wasa wurin maneman auren ta?...gaskiya dole mu mike tsaye..." Wata babban cikin su ta fada , Dan tsayawa nayi na kurawa dukkan su kallo naga suna dan kama da juna da alaman dukkan su biyar a related ko kuma ince are siblings. Matan gidan kallon wacce tayi magana tayi
"Sisters... Kar muyi staining hannuwanmu da zunubai kan matsalolinmu...yanzu in mukaje wurin malamai..abubuwa daban2 zasu fara fada mana....kawai mu kai kukan mu ga Allah batare da Mun je wani wurin ba...." Mikewa babban cikin su tayi
"Ki zauna nan ...ai kin ga zama...." Tafada tana daukan wani hadadden hand bag tare da Vail da ke kusa daita, kallon ta Matan gidan tayi ta kalli wata mai aiki dake jera abinci kan dinning Sannan tace
"Anty ki zauna ki ci abinci mana..." Matan galla mata harara tayi
"Ke Allah ya sauwake halin ki....wato ta abinci kike?...mtssss" ta fada ta bar sauran nan zaune. Hanyen waje tayi. Matan gidan mikewa tayi jiki ba kwari ta dan raka Matan Sannan ta dawo. Sauran mikewa sukayi Tana karasowa cikin falon ta kalli sauran Matan Sannan tace
"Sisters.. Muje muci abinci..." Tafada cikin sanyin murya, dukkan su mikewa sukayi Sannan daya daga cikin su tace
"Ina ihsan din take?..."
"Tana upstairs..." Matan gidan ta amsa mata. Wacce tayi tambayan ta kama hanyan upstairs sauran suka nufi kan dinning table.

A upstairs kam cikin daya daga cikin dakunan wasu beautiful black beauties biyu ne zaune kan gado, daya bata da Dan kwali tana zaune kan gado don har kafafunta suna kan gadon, da ganinta cikin tunani take, daya kuma zaune bakin gadon hannun ta daya kan cinyan wacce ke zaune kan gadon,
"Babe am so sorry about this... Kiyi hakuri..Allah zai baki Wanda ya fishi..." Inji wacce ke zaune bakin gadon, itadai bata ce komai ba don banda tunanin rayuwan ta babu abinda takeyi, tacigaba dacewa
"Shahid doesn't deserve you... Ki kwanta da hankalin ki Allah zai kawo Wanda ya fishi..." Tafada tana massaging yatsunta Ahankali, Ahankali yarinyan dake zaune kan gadon ta daga manyan idanuwanta Sannan tace
"Ni har yanzu abinda ke bani mamaki shine duk basu cewa ga laifina agaresu...ko jiya kwana mukayi da shahid...amma..." Bata idaba ba kuka ya kufce mata
"Sis what have I done wrong?... What is happening to me?...in one year... 3 wedding date amma non is coming through..." Tafada cikin kuka sosai, da sauri dayan budurwan ta haye kan gadon, ta rungume ta tana cewa
"Babe...please don't cry...you know how much I hate to see you cry...please stop it...." Tafada cikin comforting tune, itakam kaman ance ta ta kara volume, rungume kawarta tayi ta cigaba da kuka,
"In kina kuka ni ince me?...remember we are of the same age amma babu namijin da ya taba kawo kudin Neman aurena gidanmu... So kinga yours is better..." Da sauri mai kukan ta fara girgiza kanta tana cewa
"Wallahi naki ya fi....nida sai ansa rana an kawo lefe sai a fasa fah?... Yanzu mutane sai suyita tunanin wani mugun Abu nakeyi yasa ake guduna....Wallahi am tired...." Da sauri kawarta ta rufe mata baki tana cewa
"Shhhh....stop saying that...komai jarabawa ce...Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawan...." Bata idaba ba wayanta ya fara ringing, da sauri yarinyan dake kukan ta daga kanta tana kallon wayan kasancewan tasan mai kiranta cos he's ringing tune is different, itama kawarta kallon wayan tayi, ihsan zata dauki wayan kawarta tayi saurin daukan wayan tayi picking tafara cewa
"Munafiki...Allah yaisa tsakanin mu da kai...wallahi yanda ka sa aminiyata hawaye kaima sai kayi Wanda yafi nata.... Shege...." Tana kaiwa nan ta katse wayan, ihsan tsaya kallon ta tayi,
"Haba husna....what did you do that for...." Da sauri ta fara cewa
"Yo ai is better in zage shege....in badan ya rainaki ba ya zaayi ya fasa auren Sannan ya kiraki Dan uwarshi...."
"Kilan hakuri zai bani..." Tafada ahankali,
"Kam...Allah ya sauwake..." Bata idaba wayan ya dauki ringing kuma da sauri Husna ta dauki wayan ta kashe shi ga baki daya, itakam ihsan bata kara cewa komai ba tacigaba da kukan bakin cikin abinda ke damunta, itakuma husna sai lallashinta take, kofan dakin aka bude wata ta shigo
"Ambaby Ashe haka aka karayi?..." Matan ta fada, da sauri ihsan ta mike ta fada jikin mata ta kara fashewa da kuka,
"Kai...stop crying... Meye abun kuka?....." Inji Matan,
"Abinda nake fada mata kenan anty Zainab..." Inji husna
"To kinji kawarki ta fiki ahankali... Ki shuru abinki.. Meye cikin auren in badan yana sunnan manzo ba...." Anty Zainab ta fada tana shafa bayanta,
"Amma anty kilan aljanu gareni...."
"Shush...ki bar fadan haka...komai daga Allah ne...ko aljani sai da izinin Allah.... Maza muje ki ci abinci..." Da sauri ihsan ta girgiza kanta
"Anty ban iyacin komai..." Anty Zainab Dan tureta tayi tana cewa
"Ki sauko kici abinci in ba haka ba in kira maki anty Zuwairat..." Da sauri ta kalli Anty Zainab
"Ta zo ne?...."
"Eh..tana downstairs..." Da sauri ta goge hawayenta tare dashiga bathroom ta wanke fuskan ta ta fito amma still idanuwanta ja ba kaman kasan idanuwanta abinda da farar yarinya.
"Babe muje muci abinci..." Ta fadawa husna cikin sanyin murya dukda tasan ko kadan ba abincin zata iyaci ba amma tana tsoron anty Zuwairat don duk cikin yan uwan mom tafi tsoron ta cos she's a no nonsense person. Dukkan su fitowa sukayi.
Suka zauna kan dinning, mom sai kallon ta take, duk mutane sai cin abinci suke amma banda ihsan dake wasa da spoon dinta,
"Wai baki cin abincin ne?..." Wata mata ta daka mata tsawa da sauri ta fara cin abincin, da gani Matan itace anty Zuwairat, itakam husna ko daga kai bata Iya yi don ba karamin tsoron anty take ba.

Haka ta dinga forcing kanta tana cin abincin har ta dan koshi, gyara kan dinning sukayi itada husna tare da mai aikin su, hanyan upstairs sukayi tare mom ta kirata suka koma falo. Kallon indian movies suke amma hankalin ihsan bai waje duk ta fada duniyan tunani, hannun ta husna ta kama kasancewan zaune suke kusa da junansu , mom kam banda kallon yarta babu abinda takeyi, around 3:30 su yan uwan mom suka zaunar daita suka bata shawara kan ta kwantar da ta dinga adua, jinsu kawai take don tasan she's lazy in the aspect of praying, Sam bata iya daukan good 30 minutes tana gamawa da Allah, ko sallah kullum in tana yi kaman ana jiran ta, mom har tayi mata fada ta gaji kan rashi aduan ta bayan ta idar da sallah.
Bayan sun gama bata shawara sukayi bankwana da mom Sannan suka tafi. Bayan tafiyan su da yan minutes wani Prada ya shigo gidan, wani babban mutum ne aka budewa kofa ya fito, da kanshi ka ga mahaifi ihsan don har idanuwansu iri daya. Yana shiga falo husna ta ruga da gudu ta fada jikin shi ta fashe da kuka, mutumin rungume ta yayi yana shafa bayanta yana cewa
"Haba momina... Stop wasting your tears...nobody is worth it... Ki bar kuka kinji momin daddy...." Bai idaba wasu yara uku suka shigo ciki da alaman daga school suke don sanye suke da school uniform, suma rungume mutumin Sannan babban cikin su wacce zata kai shekara sha hudu tace
"Yaya ya akayi idanuwanki suka kumbura?... What's wrong with you?..." Ahankali ihsan ta kama hannun yarinyan Sannan tace
"Janna...shahid ya fasa auren...." Tafada wasu hawayen suna zubowa, dan buga kafa janna tayi tana cewa
"But why?...me kika yi mashi?... Wallahi duk na fadawa class mate dina...ohhhhh my Allah..." Duk abinda sukayi mom na zaune tana kallon su haka itama husna, karamin cikin su Wanda bazai wuce 8 years ba yace
"Yeyyyyy...daman banason yaya tayi aure...kullum adua nake kar ta tafi ta barni gidan nan...I always want her around me...." Hannu Janna ta daga zata huge ta ihsan ta rike mata hannu
"Yanzu handsome bakasan inyi aure?...remember am 20..." Yaron daga mata kai yayi alaman eh wato da gaske yake,
"To shikenan... Sai in zauna ka dinga kallona...." Tafada cikin sanyin murya,
"Yeeyyyy daman haka nakeso...after ga bestie dinki batayi aure ba..." Yafada yana nuna husna nake karasowa wurin dad ta durkusa ta gaidashi ya amsa mata cikin jindadi don kowa na gidan suna kaunan husna tamkar yanda suke kaunan ihsan.

Mom ce ta mike ta rike hannun mijinta ta kaishi part dinshi, yan makaranta su ka hau upstairs don cire kayan school.

Around 6:00pm husna ta kalli ihsan Sannan tace
"Babe zan wuce..." Da sauri ihsan ta kama hannun ta Sannan tace
"Pls babe kar ki barni....wallahi I want you around me...banason ki barni..."
"Bari in fadawa mom tunda ba fada mata zan kwana ba...." Ta fada tana dailing number mom dinta
"Ok.." Ihsan ta masa mata, bayan kaman few seconds akayi picking call daga chan bangaren, husna ta fara cewa
"Momcy..zan kwana gidansu ihsan... Gobe zan dawo...." Daga chan bangaren matan tace
"Ok...gobe zanzo gidan sai mu taho tare...ki gaida min su..."
"Ok momcy..." Tafada Sannan ta katse wayan ta
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: ❤💜💚🖤💛💙
KAWARTACE SANADI
💚💛💜🖤💙❤

®zuwairat( ummu Maryam)


2⃣


Gidaje biyar daga gidansu ihsan kam wani babban gida ne Wanda mai gadi ya bude gate adaidai lokacin da wani babban mota Wanda aka rubuta GMC ya yi horn gaban gidan. Mai gadin yana budewa yana gaida Wanda ke cikin motan, hannu kawai ya daga mashi Sannan ya shiga cikin compound tare da parking cikin parking lot inda sauran cars suke, bayan ya gama parking yayi relaxing cikin motan for about 5 minutes Sannan ya fito, hmmm am dropping dead cos gayen is beyond handsome, gashi ko kadan ba fari bane, sanye yake da jean da normal t shirt, hannun shi kwance take da gashi don tamkar ayi kitso, a babban yatsanshi silver ring ne mai shegen kyau da tsada, daka ganshi kasan he's tired, bayan ya fito ya zagaya baya ya dauki bag dake dauke da something like system Sannan ya rufe motan ya fara takawa ahankali, gani nayi ya nufi wani part ba mai girma ba don da akwai babban apartment amma Wanda ya nufa is moderate, yanda yake tafiya kama bata lakka ajiki,
"Yaya Ayan!...." Wata yarinya ta kwala mashi kira daga benen babban apartment, daga kai yayi ya kalle ta,
"Babyna... Ya kike..." Yafada har lokacin yana tsaye, yarinya wacce bazata wuce 15 ba tace
"Am fine...ya aiki?..."
"Alhamdulillah... Hope you took very good care of Umma?..."
"Yes yaya..."
"That's good... Bari in watsa ruwa...."
"Alright yaya..." Ta amsa mashi, ahankali yacigaba da tafiya, bai ida kaiwa bakin kofan ba ya karajin ance
"Yaya Ayan... Welcome..." Daga kai ya karayi ya kalli wasu yanmata biyu da ganinsu kasan yan biyune,
"Yauwa...how was your day?..."
"Fine yaya..." Suka amsa mashi in chorus
"Ya lectures?..." Ya kara tambayan su
"Cool yaya..." Suka kara masa mashi in chorus
"Good.. Let me take a shower...." Yafada masu Sannan ya karasa bakin kofan, ya bude ya shiga. Falon yana da kyau sosai kaman bana saurayiba, one bedroom apartment ne, tun daga falo ya fara cire kayanshi, daga shi sai boxer shorts ya shiga bathroom ya sakar wa kanshi ruwa Sannan ya fito daure da towel. Light kaya ya saka don he don't mind walking naked no dukda kayan daya saka basu da nauyi ji yake kaman da dutsi cikin su. Wayanshi yadauka ya saka cikin aljihunshi Sannan ya fito ya nufi babban apartment din. Yana shiga falo wata babbar mace ta daga kai ta kalleshi, da sauri wani yaro dake zaune gabanta ya taso da gudu
"Yaya...oyoyo..." Yafada yana makale shi. Ayan daukan yaron yayi ya daga shi sama Sannan yace
"Superman...how far..." Yaron Wanda bazai wuce 10 years ba ya amsa da
"Am great yaya..." Karasawa yayi wurin Matan ya zauna
"Umma ina wuni..."
"Alhamdulillah son ya aiki?..."
"Lafiya lau...ina Abba naga motanshi a parking lot..." Yafada yana relaxing kan sofa
"Maza tashi kaci abinci... Don't relax...." Inji Umma, ta fada tana tureshi daga kan kujeran.
"Ohhh Umma am tired ..I want to rest...." Ya fada cikin shagwaba, yaron dake zaune kan kafan Umma saida yayi dariya
"Da akwai patient da yawa a hospital yau ne?.." Umma ta tambayeshi
"Yes Umma..."
"Ko zaka kara doctors ko nurses?..."
"Umma ba karancin doctors ko nurses bane kawai wannan season da koina rashin lafiya ne, baka minti biyar zaune sai an tqdaka...." Yafada yana Kara relaxing

"Eat then you rest...." Inji Umma, yana kokarin nufan kan dinning da aka jera abinci na daidai mutum daya.

Yanbiyu suka sauko,
"Umma zamu he ganin lefen ihsan..." Inji daya daga cikin yanbiyun,
"Ok...nima gobe zan shiga...." Inji Umma,
"Salma!..." Ayan dake zaune kan dinning ya kira daya daga cikin yanmatan
"Yes yaya..."
"Pls serve me before you go..." Yafada mata cikin kasala, da sauri yarinyan daya kira ta je tayi serving dinshi Sannan suka kama hanyan waje
"Ku dawo yanzu..magrub is around..." Umma ta fada masu
"To Umma .." Suka fada Sannan suka fice. Wata yarinya ce ta zauna kusa da Ayan ta fara feeding dinshi yana amsa abinci suna hira, bayan kaman minti talatin da fitan yanbiyu suka dawo.
Yanayin fuskan su said it all
"Lafiya na ganku haka kaman ku dawo daga gidan mutuwa?.." Inji Umma, shikam Ayan juyowa yayi ya kallesu don har lokacin bai tashi daga kan dinning ba dukda ya gama cin abincin. Jiki ba kwari ya yan biyu suka zauna kusa da Umma, Ayan sai kallon su yake don yana tunanin kilan wani ya bata masu rai yayi rashin mutunci
"Wai ba daku akeba?..." Ya daka masu tsawa, ahankali daya daga cikin yan biyu ta fara cewa
"Wai Umma an fasa bikin ihsan...."
"Subhanallahi... Not again..." Inji Umma, Ayan najin abinda suka fada ya juya don baisan inda zancensu ya dosa ba, hira suka cigaba dayi da little sis dinshi mai suna hafsat, Umma kam sai mamakin abinda yan biyu suka fada mata take,
"Har muna murnan da akwai shagali a nan President avenue tunda sati two ke tsakanin nata da namu....amma gashi an fasa kuma..." Inji salma,
"Ni wallahi abinda ke bani mamaki shine ko kadan ihsan bata da halinki....I don't know why this is happening to her...." Inji gudan yan biyu mai suna samera, Umma dai shuru tayi don tunani kawai take
"Ni wallahi kwata2 ihsan bata da wani bad character..ina Iya shaidanta tunda course mate ditace..." Inji salma,
"Samera daukomi gyale daga upstairs..." Inji Umma cikin sanyin murya, da sauri samera ta haye sama baa dadeba ta dawo da wani expensive Vail ta mikawa Umma, amsa Umma tayi ta yafa, da sauri Dan karamin yaron ta ta mike
"Umma zanje...." Yafada kaman zaiyi kuka
"Lets go..." Tace mashi, Ayan juyowa yayi
"Umma ina zaki?..." Ya tambayeta
"Nan neighbor zan shiga..."
"Ko in rakaki tunda magrub ta gabato?.." Inji Ayan
"No..ka huta...yanzu zan dawo..." Tafada tana kama hanyan waje autanta da biye da ita. Part din Abba sukaje ta fada mashi abinda ke faruwa, shima mamaki ya dingayi don suna mutunci sosai don basu sati basu nemi junansu ba dukda busy schedule dinsu.
" I think wannan shine kashi na uku ko?..." Abba ya tambayi Umma
"Eh Wallahi... Wannan abun yayi yawa..." Inji Umma
"Allah ya kawo mafi alkhairi..." Inji Abba
"Ameen... Bari in leka chan..."
"Ok...bari in kira Musa.." Abba ya fada yana daukan wayanshi. Umma fita tayi superman yana biye dashi.

Kanwar Ayan wacce ta bashi abinci yaci my suna Nafisat amma ana kiranta antynmu cos sunan babban kanwar Umma aka mata ta dauko assignment, suna zaune nan kan dinning table yana nuna mata assignment din, yana gamawa ya mike ya nufi part din Abba, cikin respect ta gaidashi as usual Sannan ya fara cewa
"Abba..." Ya kirashi cikin sanyin murya
"Yes son...." Ya amsa mashi
"Daman inason ka bani izini in koma cikin wannan gidan tunda an gama...." Ya fada kanshi kasa, kallon shi Abba yayi for a moment
"Meye dalilin ka nason barin wannan gidan...."
"Babu wani dalilin... Kawai dan yafi kusa da hospital...." Yafada Ahankali, kai Abba ya girgiza Sannan yace
"Wannan ba dalili bane...anyway ka bari Sai kayi aure..." Da sauri Sadiq ya kalleshi
"Abba yanzu sainayi aure zan koma ?..." Ya tambaya har cikin ranshi bai so hakan ba,
"Eh..ko da akwai wani abu daban da kake na niyyan yi?...." Da sauri ya girgiza mashi kai
"Good... " yafada yana mikewa, Ayan na zaune wurin har Abba ya fito daga bathroom, shima mikewa yayi ya shiga ya dauro alwallah Sannan suka fita zuwa masjid, Suna isa bakin gate Umma da Ismail wanda suke kira da superman suka dawo, da gudu yaron ya tafi bakin tap dake bawa flowers ruwa ya dauro alwallah Sannan suka tafi gabadayan su.The following day Ayan ya shirya ya ajiye antynmu da ismail a school Sannan yawuce wurin aiki.

A hospital kam yana zuwa wasu guys guda biyu suka nufoshi,
"Fabulous.. How far Abba ya amince?..." Daya daga cikin su ya tambayi Ayan,
"Wallahi guys Abba bai amince ba...wai Sai nayi aure...." Dariyan rainin hankali gayun biyu sukayi Sannan farim yace
"Kambu...kai yaushe zakayi aure?... Ko baby fa baka dashi...." Dariya suka karayi, ba kara kallon suba ya sa mukulli ya bude office dinshi still suka biyo shi,
"Wallahi fab naso muyi rocking wannan gidan kafin kayi aure..,"
"Ka rungumi sorry ..." Inji Ayan dake fiddo laptop dinshi daga cikin bag, duk guys din sunyi mashi tsaye, zama yayi yana kallon su
"Ya akayi ne?..." Ya tambayesu, kallon juna guys din sukayi Sannan daya yace
"Ka nemo mana wata mafitan....we need place to party..." Galla masu harara yayi
"Ku tafi bakin aikinku ko inyi saking dinku yanzu nan...." Yafada in am the boss voice, dariya sukayi tare da tafawa Sannan sukace
"Yes boss..." Suka fada Sannan suka fita


Abangaren ihsan da following day ta shirya sisters da brother dinta tare da taimakon husna suka rakasu har inda suke hawan school bus Sannan suka dawo gida, har yanzu bata bar tunanin matsalan rayuwan ta ba, suna daf da shiga gida wani mai mota ya dinga horn, bata juya ba sai husna data juya ta kalli saurayin dake cikin motan,
"Baby kizo mu shiga cikin gida...." Inji ihsan, cikin whisper husna tace
"Ke bari inje...kikasani ko nawa mijin ne?.." Tafada Sannan ta juya ta koma wurin mai motan itakuma ihsan ta shige gida. Husna na zuwa wurin saurayin suka gaisa Sannan saurayin yace
"Dan Allah yanmata wancan yar uwarki ce?..." Ya tambayeta , nan take yanayin fuskanta ya chanza.
"Ya akayi?..." Ta tambayeshi fuskan ta kaman bata taba dariya ba
"Tayi min ne...." Dan baki ta tabe Sannan tace
"Ka fada mata...." Tana kaiwa nan ta juya , dasauri saurayin yace
"To Dan Allah ki kiramin ita...." Banza tayi ta shige cikin gidan su ihsan ba tare data amsa mashi ba, cikin kitchen ta tarda ihsan tana jerawa mai aiki abinci kan tray ta kai kan dinning, juyowa tayi ta kalleta
"Har kin gama zancen?..." Ihsan ta tambayeta, lafiya lau tayi dariya kaman ba itaba Sannan tace
"Ke rabu da dan iska..." Dariya ihsan tayi
"Ke kullum wurin ki samari yan iska ne...yanzu me ya fada maki har kika maidashi Dan iska?..." Inji ihsan,
"Babe kawai dan iska ne..." Ta amsa mata atakaice. Breakfast sukayi gabaki dayansu banda sauran yaran dake school da dad dake tafiya da breakfast dinshi office, mom na gani yanda ihsan ta Dan saki jiki ta ci abinci kaman ba ita ba ta kalli husna Sannan tace
"Second daughter ina gode maki....you have always been there for your friend...da bansan yanda zanyi daita ba in babu ke ...na gode Allah yayi maki albarka..." Kanta kasa ta amsa da
"Ameen..." Ihsan kama hannun ta tayi tace
"Thanks for been there for me..." Harara husna ta galla mata Sannan tace
"Nasan ke in ina cikin matsala zaki taimaka min...so.is nothing..." Suna gama breakfast suka gyara gidan kaman yanda suka saba don duk ranar da husna tazo gidansu ihsan da ita suke aikin gidan haka itama ihsan in taje gidan husna tare suke aikin gidan su. Shakuwansu ta wuce misali, unfortunate twins ake kiransu tunda daga primary school har zuwa yanzu da suke 300 level a buk, amincinsu ya sa iyayensu aminci, amma one thing is that ba halinsu daya ba, ita ihsan is straight forward, bata da fuska biyu while ita husna is a very good pretender

Abinda fuskanta ke fada daban da abinda ke cikin zuciyanta, kuma nobody knows her true colour, ko uwarta batasan real halinta ba, amma kunsan ko wane hali na da inda aka samo shi dukda ba duka halin iyaye yara ke inheriting ba amma some of children's characters a inherited from their parent. In kana abu to confirm da akwai dan da zaka Haifa ya fika wajen wannan abun. Allah yasa mu dace ameen.


Bayan sallan zuhr Hajiya amina wato mahaifiyar husna ta zo gidan. Lokacin su ihsan da mom na zaune falo, tana sallama ihsan da husna suka mike da gudu suna rige2 isa gareta, rungume ta sukayi har suna neman kadata,
"Mami sannu da zuwa..." Suka fada mata a tare
"Yauwa yan biyun mami..." Tafada tana rungume dasu biyu, mom kam dariya take tana cewa
"Ko yaushe zaku girma?..."
"Ki kyale manisu tunda ni bani dasu da yawa..." Inji mami kasancewan yaranta biyu duk mata, daga husna Sai kanwanta Fiddausi.

Zama mami tayi suka gaisa da mom har lokacin su ihsan na makale da ita,
"Mami ina tsarabanmu?.." Ihsan ta tambayeta,
"Ku duba cikin handbag dina baku rasa abin lasa..." Ta fada tana ajiye masu handbag dinta, da sauri su biyu suka suri bag din suna dubawa, husna ce ta dauko orbit gum da kingtat chocolate, tana daukan su tayi sama da gudu
"Kam.. Ai wallahi kinyi kadan..." Inji ihsan dake biye da ita da gudu, mom da mami ban da dariya babu abinda sukeyi.
Mai aiki mom ta kira ta kawowa mami abin sha. Daga nan hira ta barke tsakanin su
"Oh ni ameenatu...INA mamakin wannan ikon Allah.... Ashe duk Sai su kawo lefe su fasa auren..." Inji mami dake jimamin abinda ke faruwa
"Aikam hajiya" tagumi Hajiya ameenatu tayi for a few minutes Sannan ta mike ta koma kusa da mom, mom dan gyara zamanta tayi don ta samu daman fuskantan Hajiya ameenatu, cikin magana kasa2 Hajiya ameenatu ta fara cewa
"Yanzu Hajiya wace mataki kika dauka?..." Tafada yanda babu mai ji Sai mom, ahankali mom tace
"Hmmm yaruwa adua kawai muke... Komai yayi farko dole zaiyi karshe Sannan duk nisan jifa kasa zai dawo...." Ido mami ta zaro
"Kambu...adua!?..." Ta fada sounding as if mugun abune adua Sannan tacigaba dacewa
"Wa ke tsaya adua yanzu?... Ai Sai a gama da kai kafin aduan taci...." Tafada sounding discourage
"To hajiya in ba adua ba mene abinyi?...Wallahi right now am so confuse...." Yanda tayi maganan ya nuna da gaske she's feed up with her daughter's predicament, hannun ta mami ta rike Sannan ta fara cewa
"Kinsan Hajiya Hadiza tamkar yar uwa na dauke ki...dukda ta sanadin yaranmu Allah ya hada mu..bazan ga abinda zai cutar da ke inyi shuru ba mussanman ihsan cos tamkar husna na dauketa....ina da wani malami a hotoro muje muji actual abinda ke faruwa...." Tunda mami ta ambaci malami mom ta bude baki tana kallon ta, don banda mamaki babu abinda take, Ahankali ta daga mayyan idanuwanta Wanda ihsan ta gada ta kalli mami Sannan tace
"Hajiya na gode da damuwanki kan matsalan mu amma gaskiya I don't want to go astray..." Kallon mamaki mami tayiwa mom don batayi tunanin zatayi gardama with the problem she's having ba
"Amma Hajiya ba going astray bane....kinga wannan yarinyan tana bukatan adua daga manyan malamai don abinda ke faruwa ba haka nan bane....in baki zuwa ki amince Mani in tafi daita wurin malamin ya duba mani ita....pls don't refuse me..." Tafada har lokacin tana rike da hannun mom yanda take magana tamkar itace mahaifiyar ihsan,
"Wannan Matan bata da hankali...yata takeson koyawa bin malamai tun yanzu?...Allah yasa bata koyawa yarta ba din in haka ne to da akwai matsala..." Mom ta fada cikin ranta, azahiri kam murmushi tayi tare da dora hannun ta daya kan hannun mami dake rike da hannun ta Sannan tace
"Hajiya babu Katanga tsakanin mu da Allah... Nasan ba kasafai adua keci da wuri ba amma mahakurci mawadaci....don haka abinda nake bukatan ki yiwa yarki ihsan shine ki taimaka mata adua...with Allah Almighty all things are possible.... Nasan in mijinta yazo babu abinda ya isa ya rabasu...." Mami kallon ta ta tsaya yi, batace kala ba saida ta kai aya Sannan tace
"To shikenan....Allah yasa mu dace...." Tafada batare dataji komai ba,
"Ameen... Uwar ihsan da husna...." Inji mom. Hira suka cigaba dayi har bayan asar Sannan suka shiga mota da husna ta jasu suka bar gidan.
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💙💚💜🖤💛❤
KAWARTA CE SANADI
❤💛💙🖤💜💚


®zuwairat( ummu Maryam)


3⃣


Mami na tuki husna zaune gefen ta tana chatting da wayanta, dan daga kanta tayi taga mami ba hanyan gida tayi ba
"Mami ina zamu?..." Tafada tana kallon hanyan, dukda tasan inda zasu amma still saida ta tambayeta
"Gidan Malam..." Ta amsa mata atakaice,
"Ba last week muje ba?..." Kallon su nayi ina mamakin abinda ke faruwa, wato uwar da dayartatake zuwa gidan Malam,
"Eh...kudi zan kai mashi don naji dadin aikin da yayi min..."
"Ok..." Husna ta fada tana relaxing cikin motan tare da cigaba da chatting.
"Baby...." Mami ta kirata, ahankali ta daga very beautiful and innocent face dinta ta kalleta mami ta cigaba dacewa
"Matsalan kawarki yana damuna... Gashi nayiwa mahaifiyar ta magana kan muje wajen Malam kuma taki..." Dan baki husna ta tabe tare dacewa
"To mami tunda basu so na sai ki kyale su ba...." Kallon ta mami tayi kuma tayi mamakin jin irin wannan maganan a bakinta
"Baby matsalar bai damunki ne?..." Mami ta tambayeta tana karya kwana.
"Mami yana damuna mana..amma tunda basu son taimako sai a kyale su...is not by force..." Tafada in I don't care manner.
"Hmmm...I wish there is something I can do about it..." Inji mami dake parking a kofar wani tsohon gida. Yanda take magana tamkar tana magana da wata kawarta sam kama ba ita ta haifi husna ba nikam mamaki kawai nake.

Dukkan su fitowa sukayi suka shiga wannan karamin gidan, da Sallama suka shiga cikin gidan, da maraba aka amshe su don da gani Matan gidan sun saba da su,
"Ina Malam?..." Mami ta tambayi Matan gidan, babban cikin su dake shara ta kalli mami da murmushi fuskanta Sannan tace
"Ki shiga ciki...yana nan...." Mami sallama tayi bakin wani karamin kofa wani matured voice ya amsa mata, husna kam, zama tayi kan wani bench dake kofan daki.
"Kema ki shiga mana...sai kace wata bakuwa?...." Inji Matan dake shara, murmushi husna ta saki Sannan tace
"Nan ma yayi..." Ta amsa mata.

Wani babban mutum ne zaune kan katon carpet, gaisawa sukayi da mami da gani mutumin ya ji dadin zuwan mami.
"Hajiya da fatan lafiya?.." Mutumin ya tambayeta,
"Lafiya lau..daman godiya nazo in maka...Wallahi wannan aiki yayi sosai... Ya bani kudin dana bukata...." Tafada tana dariya ,shima mutumin dariya yayi
"AI bai sai kinzo ba...ko waya kikayi ya wadatas...." Inji Malam, itakam husna tana jin duk abinda suke cewa kuma babu alaman surprise tattare da ita cos daita mami ke zuwa wurin malaman ta.

"Ai ya zama dole inzo...." Tafada tana saka hannu cikin handbag dinta. Dubu 50 ta yi counting ta mikawa Malam, mutumin washe baki yayi
"Ga wannan, aikinka yayi kyau...." Inji mami,
"Hahhhh...ai kadan kenan...kudi kam sai an karo maki tunda kin kawo hasafi...." Inji Malam
"In kam alhaji ya karo kaima zakaji ajikin ka.." Inji Hajiya dake dariyan jindadi. Mikewa tayi
"Wucewa zanyi cos daman abinda ya kawoni kenan..." Shima tsohon mikewa yayi
"To nagode..." Mami fitowa tayi tsohon na biye daita,
"Kece kikazo baki shigo kin gaida Malam ba?..." Inji Malam daya gan husna dake zaune kan bench, murmushi husna tayi tana mikewa tare da gaidashi, shima amsawa yayi yana murmushi.
Har kofar gida ya rakasu suka shige mota suka kama hanyan gida.


Ihsan na kwance tayi ruf da ciki idanuwanta lumshe amma ba bacci take ba, sanye take da doguwa rigan swiss lace, sai karkada kafa ahankali bude kofan da akayi yasa ta bude ido, dan juyawa tayi ta hangi mom, da sauri ta mike zaune don mom bata fiya shiga dakinta ba.
"Habibty..." Mom ta kirata tana zama a bakin gadon ta, kai ihsan ta daga tana kallon ta, Ahankali mom ta sa hannu ta Dan cire mata strand of hair dake fuskan ta, idanuwanta mom ta kalla tana jin so da kaunar yarta har cikin ranta
"Kiyi hakuri da jarabawan da Allah ya Dora maki...komai yayi farko tabbas zaiyi karshe....kuma dan Allah ki bar wannan 3 minutes prayers... Ki dinga zama kan sallayanki kina rokon Allah...."
Raurau ihsan tayi da idanuwa,
"Kuma dan Allah in wani abu kike Wanda mu iyayenki bamu saniba to ki bari don na tabbatar ba haka nan maneman auren ki suke ja da baya ba..." Bata idaba ihsan ta fashe da kuka tana cewa
"Yanzu mom zargina kike?..." Da sauri mom ta girgiza mata kai
"Not at all... Kawai am advising you as your mother...." Mom ta fada mata tana kama mata hannu da one hand Sannan tana goge mata tears da dayan hannun ta,
"Mom wallahi ba na mugun abu... Kuma adua am trying hard sai dai bana jure adua sosai...at times I sleep of...."
"To ki kokarta ki dinga yi....sai indai wannan matsalan bai dameki ba...." Mom ta fada in a cool voice
"Ok mom...." Tafada har lokacin bata bar kuka ba, rungume ta mom tayi tana cewa
"And kar ki sake ki biyewa duk Wanda zai nemi ki kauce hanya sanadiyan wannan matsalan.... Do you understand me?..."
"Eh mom..."


After two days ta koma normal kamar babu abinda ya faru don har lectures ta fara zuwa, daman ita ihsan a rayuwar duniya bata da aminiya kaman husna, she can share anything with her, don sau da dama tana fada mata abubuwan da bata fadawa mom.


Bayan wata daya da fasa auren ihsan wani ya fara zuwa wurin ta, family sai cewa suke tana da white blood, itakam husna abun ya fara damunta don ta san ihsan bata fita komai ba amma ko suna tare da anyi horn to ihsan suke so, daman gata good pretender bata nunawa abun yana damunta amma har cikin ranta kaman ta mutu take ji don har cewa take
"Ya zaayi best friend dita tayi aure in dinga zuwa gidansu as budurwa?...AI wallahi saidai muyi tare ko kuma in rigata..." Take fadawa kanta, yanzu kanwarta da suke har maza sun fara neman tabda aure amma ita saidai suzo mata da maganan banza.

Yau ta fito daga wanka daure da towel, gaban mirror ta tsaya tare da cire towel dinta ta tsaya yanda Allah ya halicceta tana kallon kanta, komai nata kaman ita tayiwa kanta, her figure 8 is something else komai normal amma she wonder why nobody is seeking for her hand in marriage. Wayanta ya fara ringing ta duba taga ihsan, saida ta saki tsoki Sannan tayi picking,
"Hello babe how far...." Tayi magana kaman ba ita bace tayi hissing yanzu nan.

Ihsan dake zaune kan gadonta sanye da skirt and blouse na atampa tace
"Babe guest what..."
Daga chan bangaren husna ta gallawa wayan harara tare da Jan inner hiss Sannan tace
"What..." With high tune kaman da gaske
"Could you believe Mahmoud yace zai turo?..." Inji ihsan dake magana sounding extremely happy. Daga chan bangaren idanuwa husna ta zaro, she couldn't believe her ears, jitayi as if her heart will pop her ribcage, nishi ta farayi sama2, amma dayake anamimiyace sai ta sake shewa tare ea guda tana cewa
"Babe are you serious?..." Ta fada kaman da gaske

"Hmmm babe haka yace wai ya samu aiki a American embassy so zai koma chan in the next two months kuma yanason ayi aure kafin lokacin...." Tafada sounding super duper excited, husna rike throat dinta tayi don ji tayi kuka yana Neman kufce mata, kawai saita fara cewa
"Naam... Mami gani nan zuwa...." Tafada kaman ana kiranta Sannan tayi saurin cewa
"Babe...bari in kiraki mami ke kirana...." Bata sauri amsa ihsan ba ta katse wayan ta
[10/16, 5:27 PM] Re@l Zuw@ir@t✍đŸŧ: Dukan kasan tiles tayi kaman ance buga in baki trillions, duk yanda take dukan kasan ko kadan bata jin zafin hannun ta, tana dukan kasa tana kuka, kai kaji kaman komai ba na Allah bane
"Yanzu ina nan a kai kawata abroad kuma zaman aure...no way...." Tafada tana daukan wayanta, wani number tayi dailing after few seconds ta fara cewa
"Kaji aikin ya samu ..."
"Address and details..." Wani katon murya ya fada daga chan bangaren
"I will email you..." Ta fada tana kashe wayan ta. Mikewa tayi ta kara shiga bathroom ta sake wanka, ta fito ta shirya cikin material lace dinki skirt da riga, bata tsaya kwalliya ba tafito, dakin mami ta shiga
"Mami ki bani kudin tp zanje gidansu ihsan..." Kallon ta mami tayi Sannan tace
"Ba kuna tare ba throughout jiya....kuma dazun kun hadu a lectures... Me zakiyi Chan gidan yanzu...." Ahankali husna tafara cewa
"Mom yanzu nan ta kirani wai wani yace zai turo shine zanje...." Ta fadi maganan tamkar babu abinda ke damunta,
"Wowwww...masha Allah... Har ta samu wani?...kai alhamdulillah..." Ta fada tana kallon eyeball din yarta, ahankali ta fara cewa
"Habibty kar ki damu...kema Allah zai kawo naki when the time is right...." Tafada Ahankali don rashin maneman auren yarta yana daga cikin babban matsalan, kuma yana daga cikin abinda take bawa malaman ta kudi saboda suyi mata aduan samun miji amma har yanzu shuru.
Kai husna ta dan kauda yanda mami yanda bazata ganta ba Sannan ta tabe baki. Wani pause dake kan mirror maminta umarceta ta dauko mata, dauko mata tayi mami ta dauko 1k ta bata
"Ki dawo kafin magrub..."
"Ok mami..." Ta fada Sannan ta saka kudin cikin handbag dinta.
A bangaren ihsan kam farin ciki kawai take don tafi son Mahmud kan sauran maneman aurenta, ba karamin kwanta mata yayiba, tunda ya daukota daga school ya fada mata zai aiko Sannan ya ajiyeta ya wuce, ko mom bata fadawa ba ta shiga dakin ta ta kira husna.

Jiran kiran husna ta tsayayi har lokacin asar kasancewan yau Friday da wuri suke gama lectures, sallah tayi ta sauko, batafi minti biyar da sauko wa ba sai ga husna, da gudu husna ta rungume ta
"Babe am extra happy..." Husna ta fada cikin farin ciki, da sauri ihsan tace
"Shhhhhh....kar ki bari mom taji...ban fada mata ba tukunnan...you are the first person I told..." Tafada with excitement all over her. Ko mom husna bata gaida ba suka hau upstairs suka fara labartawa, murna wurin husna kaman gidansu zaa aiko ( people beware of people with two face)..

Har adua ta dingayi mat kan Allah yasa kar a fasa wannan kaman gaske, itakam ihsan sai ameen take, cikin dabara ta fada mata inda Mahmoud ke zama, around 5:pm husna tace zata tafi, ihsan mikewa tayi don rakata, husna kallon ta tayi
"Babe ina zaki?..." Ta tambayeta kaman batasan abinda zatayi ba
"I want to escort you..." Inji ihsan, hararanta husna tayi Sannan tace
"Da wannan kayan da kika saka tun safe?..." Dariya ihsan tayi tana cewa
"Wallahi sis tunda na dawo ko ruwa ban shaba saboda murna..." Itama husna dariya tayi tana cewa
"Sarauniyar zumudi...kije da sauri kiyi shower ki fito ki rakani...kuma wallahi in kin Dade tafiyata zanyi...." Bata idaba ihsan ta shiga cikin bathroom da gudu
"Yanzu nan zan fito...." Husna tabi bayanta da harara Sannan tayi saurin daukan wayanta ta bude ta tura photo da wani guy da nake tunanin shine Mahmud. Komawa wurin ta tayi tana cewa
"Wallahi ki fito ko in tafiyata..." Ta fada da karfi, da sauri ihsan ta fito daure da towel, ko shafa batayi ba ta saka pant da bra Sannan dauko wata black jallabiya ta saka tare da yafa Vail Sannan suka sauko downstairs, a falo suka tarda mom da sauran family na ihsan, gaidasu husna tayi Sannan ta wuce, fitowa sukayi suka hau kan titin street dinsu.

Adaidai lokacin Ayan ya dawo daga wajen aiki, tun daga nesa ya hango cheeks biyu sun baje kan titi kasancewan motoci basu fiya bin wurin ba saboda residential road ne
"Ji yanda wayan nan yara suka haye kan titi kaman na ubansu...." Inji Ayan dake tuki,
Yana. Zuwa kusa dasu ya fara horning, gani yayi basu da niyyan bashi hanya, kara horn yayi da karfi, gani yayi mai material tayi kokarin matsawa ita kuma mai jallabiya ta rike mata hannu alaman kar ta matsa, sai gani yayi ta nuna mashi sauran hanyan, alokacin ihsan cewa husna tayi
"Babe rabu da ko waye.. Ba ga titi nan ba?...ko da mota goma zai wuce lokaci daya...."
"Kam...amma those gal sun raina min hankali..." Inji Ayan daya cika yayi fam, daman da frustration ya taho daga wurin aiki don yau sam bai huta ba then ga friends dinshi Wanda yake aiki waje daya dasu sun bashi haushi. Horn ya karayi kaman zai fasa masu kunne, amma hannunsu rike da juna sai tafiya suke cikin kasaita kuma abun haushi ko juyowa basu yi ba balle su kalleshi, da sauri ya tsaida motan ba tare daya rufe ta ba ya fito

Afusace ya nufesu sukam basu San yanayiba, basu ankaraba sukaji an kama
Masu hannun, dukkan su juyowa sukayi,
"Kam uban nan...." Inji ihsan, itakam husna tsaya kallon wannan handsome face tayi don tunda take bata taba ganin black guy da yayi mata kaman wannan guy ba.
Ayan kam fuskanshi kaman bai taba dariya ba ya jasu gefen titi Sannan ya fara cewa
"Titin na gidanku?..." Yafada yana nuna su one after the other, husna kam kusan sumewa tayi saboda dadin muryan shi, sai kallon cute lips dinshi take, itakam ihsan kaman ta kashe kanta don takaici, don ta sanshi, ban hararanshi babu abinda takeyi
"To ko ba titin gidan mu bane sai akace ka kama mana hannu?..." Inji ihsan tafada afusace
"Hannun banza gareki... Ke har wani hannu gareki?... Mtwwwww stupid..." Yafada yana komawa cikin motanshi,
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: ❤💛💙🖤💚💜
KAWARTA CE SANADI
💜❤💙🖤💚💛


®zuwairat( ummu Maryam)4⃣


Bin bayan shi tayi da harara,
"We're not stupid wallahi...." Inji ihsan cikin murya kasa2, abinka da mai healthy ears karaf sai a kunnen Ayan, juyowa yayi ya kalleta
"Ke baki da respect ko?...." Ya fada a afusace, ihsan sai kunkuni take, ita kuma husna bakinta bude kaman sakara,
"Be careful... Am not your mate....." Ya kara fada cikin fada, ihsan sai harararan kasan ido take mashi ita wai dole Dan me zai taba masu hannu
"Ba zagin ka nayi ba....cewa nayi we're not stupid...." Bata idaba ba husna ta kama mata hannu,
"Babe let's go..." Tafada muryan ta na cracking ita dole ta ga her crush, Ayan ji yayi kaman ya Zane ihsan don yasanta , at least ya ganta sau daya ko biyu gidansu wajen twins amma shine take ce mashi she's not stupid wato ta rama zagin daya yi mata kenan, kwafa yayi ya shiga motan shi afusace ya bar wajen, bayan gidan biyu yayi horn a kafor gidansu aka bude bashi gate, sai da ya juyo ya kara kallon su especially ihsan ya watsa mata disgusting look Sannan ya shiga gida, itama ihsan hararanshi tayi
"Babe waye wancan?...." Inji husna dake blushing, baki ihsan ta tabe tare dace jan tsoki
"Wansu su salma ne....Dan iska kawai...." Tafada tana hararan gate din. Husna murmushi tayi batare da ta bari ihsan ta gani,
"Wannan guy is mine..." Ta fada cikin ranta. Hiransu suka cigaba dayi har suka kai bakin babban titi amma duk hankalin husna ya tafi ga Ayan. Adaidaita suka tsaida husna ta hau, lokacin har an fara kiran magrub, da sauri take tafiya ta kusa zuwa kofar gidansu Ayan aka bude gidan, shine ya fito sai tare da Abba su da superman, sauri take, still Ayan bai bar hararanta ba , tana zuwa kusa dasu ta gaida Abba ya amsa batare data daga kai ba ta wuce da sauri don sam batason magrub ya tardata waje.


Sai da tayi sallan magrub ta sauko ta shaidawa su dad da mom abinda Mahmoud yace,shuru dukkan su sukayi don suna tsoron a koma gidan jiya,
Sunfi minti biyar babu Wanda yace kala cikin su, chan daddy ya kalleta
"Momina... Kinsan banason abinda zai bata maki rai...." Kallon dad dinta tayi don batasan inda ya dosa ba,
"Kin tabbatar yana sonki?..." Dad ya tambayeta cikin so da kulawa, Ahankali ta gyada mashi kai alaman eh,
"To shikenan... Zamuyi bincike kanshi ..." Inji dad,murmushi ihsan tayi
"Thank you daddy..." Tafada tana rufe fuskanta, kaman cheeks dinta dad yayi kasancewan zaune take kusa da kafanshi, mom kam murmushi kawai take tana aduan Allah yasa wannan ya zama gaskiya don in har aka samu matsala wannan Karin it will ruin her.
"Go and help your siblings with their assignment..." Mom ta fada mata. Ahankali ta mike ta fita tana tafiya cikin kasaita, one thing about ihsan is she's a good cat walker don tafiyan ta na jan hankalin mai kallon ta, at times course mate dinta suna kiranta da the lady with the most beautiful steps hakan yana daga cikin abinda ke batawa husna rai, so many times zata dinga kokarin tafiya irin na ihsan amma she can never be up to her.
Ayan kam suna dawowa daga masjid yaci abinci Sannan ya koma part dinshi ya shiga wanka, fitowa yayi daure da towel ya ya kunna kallo Sannan ya haye gado tare da daukan wayanshi, browsing ya shiga yi amma sai ya tsinci kanshi da tuna yarinyan data zageshi dazun, yasan confirm ya taba ganinta gidansu, cos ba zama yake falo ba most of the time yana part dinshi amma ya taba ganinta zata fita daga gidansu tare dasu salma, the last time daya ganta bata kai haka girma ba, ji yake inama zata shigo hannun shi for at least an hour da babu abinda zai hanashi koya mata hankali
"Hmmm she have some nerves.... Me ...stupid.... Lallai yarinya ta girma...." Yafadawa kanshi. Mikewa yayi yacigaba da abubuwan da ya saba kafin ya kwanta still daure da towel don shi ko kadan baya gajiya da daura towel, at times Umma har fada take mashi don sau da dama in zata shigo part dinshi in har batayi sallama ba da towel take tardashi, sai around ten pm ya kwanta still da towel ko boxers babu jikin shi.

The following day was Saturday so bai tafi hospital da wuriba cos bazai ajiye siblings dinshi a school ba, sai around 11am yayi breakfast ya dauki machine dinshi motobi ya fita daga gida bayan yayi ma su Umma sallama. Yana fitowa kuma yayi daidai da lokacin da sisters dinshi tare da superman sai ihsan da nata siblings din suke dawowa daga islamiyya, don da akwai wani babban islamiyya inda suke zuwa 8am to 10:30am.
Ayan na gani siblings dinshi ya saki murmushi mai kayatar da fuskan shi, Dan rage gudun machine din yayi daya karaso kusa dasu, ihsan da salma tare da sameera suke ke baya kuma itace gefen kusa da titi,tana ganin shi tayi saurin komawa the other side, twins kallon ta sukayi
"Lafiya dai ko?..." Inji salma, kanta kasa ta saki murmushin karfin hali tare dacewa
"Ba komai... " tafada kanta kasa.
Ayan na kallon abinda tayi don a lokacin ya karaso kusa dasu,da sauri superman yace.
"Yaya me zaka sayomin...." Yafada yana nufanshi, tsayawa yayi tare dacewa
"What do you want...."
"Sneakers..." Inji shi, shima kanin ihsan Wanda ake kira da handsome yace
"Uncle nima ka sayomin sneakers..." Ayan murmushi yayi don kana ganin yaron kasan kanin ihsan ne, siblings ihsan gaidashi sukayi suka wuce Sannan su ihsan suka karaso wurin da yake tsaye, kafin su salma su bude baki suyi magana har ihsan ta zame ta gefen su ta wuce, da sauri sameera tace
"Sis baki gaida yaya ba...." Chak ta tsaya tana niyyan juyowa Ayan ya fixge machine dinshi ya bar wurin, Allah ya taimake su titin ba mai kura bane da ya badesu da dust,twins kallon junansu sukayi Sannan suka kalli ihsan
"Sis wani Abu ya hadaki da yayane?..." Salma ta tambayeta, da sauri ihsan ta nuna kanta tare dacewa
"Ni?..."
"Eh mana...naga baki gaidashi ba kuma kin juyo ya tafi...." Inji sameera, dariya ihsan tayi Sannan tace.
"Ni ina nake ganin yaya balle wani Abu ya hadani dashi?...kawai hankalina ne bai nan...." Tafada sounding very free,
"Hmmm ko ma meye in yayi tsami munji...." Inji salma cikin daria , itama ihsan dariya tayi
"Wallahi ban dariya gareki..." Tafada tana dariya, da sauri ta kara cewa
"Sis na samu wani suitor kuma...." Da sauri salma da sameera suka kalli junansu tare da tafawa
"Wooowwwwww....we're happy for you..." Suka fada in chorus Sannan salma tace
"Allah yasa kar a fasa wannan Karin..," ahankali ihsan ta amsa da
"Ameen..." Cikin zolaya sameera tace
"Sai Mun rigaki sanin meye rayuwar aure...." Tafada tana rufe fuskanta, hararan ta ihsan da salma sukayi Sannan ihsan tace.
"AI ba sai kin rufe fuskanki ba...ki barsu bude ..." Tafada tana dariya,
"Ni zan zo gasaki...." Inji ihsan,dariya suka cigaba dayi.

Hira sukayi sosai kafin su kai kofar gidansu salma sukayi bankwana kan sai 4pm Sannan ihsan da siblings dinta suka wuce masu gidan
Ayan kam wani irin haushi da takaici ne ya kama shi har adua yake Allah ya hada shi da wannan yarinyan inda babu kowa ya ci ubanta, duk kawayen twins ji suke dashi dukda ba time dinsu gareshi ba amma shine yarinyan da ya tabbatar ya bawa minimum of 8 years take neman raina shi
Kuma abinda ke kara bashi haushi shine yasan tana yi mashi kallon Dan iska don ya kama mata hannu, har yanzu bai bar ganin idanuwanta a yayin da take hararanshi ba, koda ya isa wurin aiki sai da Yusuf da Mohd suka gane da akwai abinda ke damunshi, kuma koda suka tambayeshi bai boye masu ba, ya kara dacewa
"I wish I can show her some respect..." Yafada yana rolling cikin kujera ahankali, dariya Yusuf da Mohd sukayi
"In banda abinka ai wannan is normal, dan yarinya ta harareka bai kamata ya bata maka rai to such instance ba...." Inji Yusuf, hararanshi Ayan yayi
"Haka nan sai age mate din third sisters dina...." Bai idaba Mohd yace
"Second dai tunda wannan ya rasu...."
"Naji...sai yarinya da na tabbatar na bawa good fucking 8 years sai ta harareni don da kaudasu daga accident?... Da bige shegiya nayi Wallahi..." Dariya suka kara yi mashi
"There is more to this..." Inji Yusuf, hararanshi Ayan yayi
"Kodai kodai..." Inji Mohd dake dariya don ba karamin dariya Ayan yake basu ba, don ya dauki abun very serious
"Kodai kodai uwarka ko?..." Inji Ayan dake kokarin mikewa hannun shi rike da wata files, fuskanshi kaman bai taba dariya ba.
Daman masu ganin dariyanshi sai family dinshi da friends in kuma ranshi ya baci sai a kwana biyu baa gan sakin fuskan shi ba, wani lokacin Umma ta kance mashi
"Dan Allah ka dan dinga sakin fuska ba komai zaka dinga murtuke fuska ba.


_Two weeks later_


Ahankali time ke tafiya inda su dad sunyi enough bincike kan Mahmoud da family sa kuma baa gano wani mugun abu game da su ba hakan ya bawa dad daman fadawa ihsan ta sanar dashi ya turo, bayan sati daya ya turo mutanen shi inda suka zo da kudin neman aure.
Atakaice nan aka saka bikin su wata 2, aranan kam duk family suka dinga adua kan Allah ya kauda sharrin shaidan.

Ita dai ihsan ko ruwa ta sha sai ta fadawa KAWARTA don duk zancen da sukayi da Mahmoud sai ta fadawa husna ita kuma already husna ta mutu kan Ayan Wanda hakan yasa ta dinga shige mashi lokacin bikin su twins amma shi Ayan in zaa kashe shi baizai fadi yanda take in short duk yanmatan babu Wanda yake kallo, amma wurin dinner ya ga ihsan, kallon ta ya dingayi don ba Karamin kyau tayi mashi dukda sai yanzu ya nutsu ya kura mata ido, suna hada ido da ita ta kara galla mashi harara tayi da suka hada ido shi kuma yayi mata kallon zaki ci ubanki ne, abinka da munafuka duk husna tana kallon irin kallon da yake yiwa ihsan don ko kadan bata dauke idanuwanta daga kanshi, hakan yasa ta bawa kanta hakuri kan bazata kara bata shirin auren ihsan da Mahmud ba don ta riga ta gano the moment ihsan is around bazata samu Ayan ba.

Ita kuma ihsan ko daidai da minti daya bata taba kwana da Ayan cikin ranta ba cos her Mahmoud was all she want in a man.
While duk lokacin da Ayan ya tuna ihsan sai ranshi ya bace at the same time kuma yayi murmushi kona meye oho.
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💛💚❤🖤💙💜
KAWARTA CE SANADI
💙💜❤🖤💛💚


®zuwairat( Ummu Maryam)


5⃣


*Friends ina baku hakuri kan yanda kukeson shiga group dina amma contact dina tayi ful* *l Kuyi hakuri kar Ku dauki abun as wulakanci pls* .


*Masu bina private suna nema daga farko suyi hakuri* *commitment ne Duke yi min yawa* *kar suyi fushi*

*Thanks* 💋💋

Ihsan ce zaune da Mahmoud a dakin visitors sai labarin su suke,sai lokacin na kalli Mahmoud, mutumin yana da kyau ga maganan shi mai kwantar da hankalin mai sauraro, yanzu bikinsu sauran sati two, ihsan ba karamin son shi take ba don gani take tafi sonshi fiye da sauran suitors dinta.
Hiransu suka cigaba dayi har wajen asar
Sannan husna ta zo don yanzu kullum sai tazo gidan su ihsan ba don komai ba sai don in zata tafi taga Ayan Kuma dayake tana na zurfin ciki bata taba fadawa ihsan tanason Ayan ba , sallama ihsan tayi da Mahmoud suka shige ciki, suna shiga falo mom ta kira ihsan ta mika mata cup din magani as usual ta amsa ta sha tana yunkurin amai, dariya kawai husna take mata, sama suka hau suka sha hiransu har lokacin da husna take tunanin Ayan ya kusa dawowa ta mike ihsan ta yafa Vail dinta suka fito.

A bangaren Ayan kam kullum kara cika yake saboda irin kallon rainin hankalin da ihsan take mashi, yanzu ya fara lura daita don yanzu kusan kullum sai ya ganta tare da wata Kuma in har ya kuskura ya hada ido daita sai ta harareshi, kullum kara jin haushin ta yake don wani lokacin ji yake kaman ya tsaida motan ya ci ubanta,
"Who do she think she is..." Ya fadawa kanshi yana shiga street dinsu,
"Mttsssss...why am I talking about her..." Ya fadawa kanshi again sounding very restless, daga nesa ya hango su biyu as usual
"Talk of the devil...kullum yara cikin yawo cikin unguwa..." Yafadawa kanshi,

Daga nesa suka hango motanshi
"Ga dan iska chan ya taho..." Inji ihsan, hararanta husna tayi batare data barta ta ganta ba, chan kasan ranta wani irin sanyi taji data hangi motan Ayan,
"Wai babe baki mantuwa ne..." Ta fada muryan ta na cracking, kallon ta ihsan tayi
"Meyasa muryan ki yake rawa?..." Ihsan ta tambayeta,
"ba komai", ta amsa mata Sannan tacigaba dacewa
" Abu kasa wata nawa amma baki mantaba?... " inji husna,
"AI abun ne da ban haushi...haka nan ya kama mana hannu..."
"Hmmm sis AI bake kadai ya kama ma hannu ba...remember harda ni...." Baki ihsan ta tabe
"AI naga abun bai bata maki rai ba amma ni ji nake kaman inyita zabga mashi mari wallahi..."
",in your dreams..." Inji husna, ahankali suke tafiya inda shima ya taho yana tukin shi cikin natsuwa, ko kadan ba daga kanshi na don bayason abinda zai bata mashi rai a wannan yamma. Amma as he drives closer to them he became anxious,
"Kilan yau bazata harareni ba..." Yafada cikin ranshi, yana zuwa daidai da inda suke ya Dan daga kanshi ya kallesu aikam kaman tana jira ta galla mashi harara tare dacewa
"Dan iska...." Dukda Ayan baiji abinda tace ba yasan dan iska tafada cos yaga movement din lips dinta
"Kambu..." Yafada zuciyanshi na har bawa da karfi, har ya wuce su ya tsaida motan kan tsakiyan titin kasancewan hanyan ba busy road bane, ihsan na ganin ya tsaida mota ta fara sauri, husna kam juyowa tayi tana kallon shi amma kaman babu kowa wurin yake gani don hankalin shi na kan ihsan
"Ke uban me nayi maki kike zagina!...." Yafada afusace, gaban ihsan mugun faduwa ya farayi amma bata juyoba, kawai kama hannun husna tayi don su kara sauri, da sauri Ayan ya tari gabanta
"Am talking to you..." Yafada yana dungurin goshinta, da sauri ta bige mashi hannu, itakam husna kusan mutuwan tsaye tayi cos ba karamin kwarjini yake mata ba.
"Ina wuni..." Husna ta fada mashi amma ko jinta baiyiba don ya tsaya yana kallon irin courage din ihsan, kokarin wucewa ihsan ta karayi ta gefen shi still hannun ta rike dana husna yakara tare hanyan
"I said uwar me nayi maki kike zagina...." Ya Kara daka mata tsawa, Dan juye2 ihsan tayi don ganin in da maizuwa don ba karamin tsoron shi takeji ba amma street din wayam babu alaman mutane
Bata amsa mashi ba ta kara kokarin wucewa
"I said why the fuck are you insulting me?..." Ya fada afusace, at the same time yana kara dungurin goshinta, wannan Karin daga manyan idanuwanta tayi ta kara hararanshi tana cewa
"Banso...ka bari...Wallahi in...." Bata idaba ya tsinka ta da mari, da sauri husna taja da baya, wani irin kara ihsan ta saki don tunda uwar data haifeta bata taba jin irin azaban dataji ba
" I said ubanme nayi maki kike zagina...." Yakara daka mata tsawa,
"Haba Malam...." Husna ta fara fada
"Shut your dirty pit...." Ya dakawa husna tsawa nan take taja bakinta ta tsuke, itakam ihsan kuka ta farayi tana cewa
"Allah yaisa...Kuma sai...." Hannu ya kara dagawa tayi saurin durkusawa don ta lura da gaske yake, tana daga durkushen ta nunata da Dan yatsa ya fara cewa
"Daga yau in kika kara daga stupid eyeballs dinki kika kalleni balle ki harareni...sai na koya maki hankali.. Am not your mate...idiot..." Yana kaiwa nan ya juya, da sauri ihsan ta mike ta koma gidansu da gudu,
"Babe kiyi hakuri... Ni zan tafi tunda magrub ta gabato..." Inji husna ...." Ko sauraron ta ihsan batayi ba ta wuce Ayan da gudu ya bi bayanta da harara ita kuma husna takama hanyan bakin titi.

Kuka ihsan ta dingayi har ta kai bakin kofan gidansu, to Ayan surprise sai taga ta shiga cikin gidansu nan gabanshi ya fara faduwa don a tunanin shi gidansu zata.
Da sauri ya shiga mota ya juya kan mota ya koma cikin gari.

Ihsan tana kuka tayi sallama kofar falon su, anci saa Umma tana zaune da Ismail, amsa sallama Umma tayi, ihsan shiga falon tayi har lokacin bata bar kuka ba
"Subhanallahi!...." Umma ta fada tana mikewa tsaye tare da nufo ihsan dake shigowa tana kuka
"Lafiya...what happen?... Me yasameki?..." Ta jero mata questions tana riketa, cikin kuka ihsan ta fara cewa.
"Yaya ne ya mareni...Kuma.... banyi mashi.... komai ba...." Idanuwanta Umma ta zaro
"Mari!..." Tafada afusace, zaunar daita tayi ta fara goge mata hawayenta,
"Kiyi hakuri... Bari zai shigo yanzu nan... Gabanki zan rama maki...." Inji Umma dake goge mata hawaye wasu na biyo baya, sun kai minti biyar babu alaman Ayan har lokacin Umma bata bar rarrashin ihsan ba. Wayanta ta dauka tayi dailing number Ayan, Ayan dake tukin mota yaga kiran Umma ya dauki wayan yayi picking yayi sallama sounding neutral kaman bashi bane yayi laifi, Umma bata amsa sallaman shiba ta fara cewa.
"Dan ubanka kana ina?..." Murmushi Mara fitowa yayi
"Ina office Umma..."
"Kaci ubanka da office... Maza2 yanzu nan ka iso gidan nan kafin ranka ya baci ....Mara hankali kawai..." Tana kaiwa nan ta katse wayan ta, Ayan kallon wayan yayi Sannan ya kara juya kan motan yana cewa
"Kam Allah yasa ba gabanta Umma ta kirani da Mara hankali ba...yarinya ta kara jin dadin raina ni...anyway ta raina ni in gurguri kan ubanta wallahi...." Yafada yana kama hanyan gida don har yayi hanyan gidan su Yusuf.

Hakuri Umma ta dinga bawa ihsan, itakam zama tayi tana jiran zuwanshi Umma ta rama mata marinta amma bai zo ba har aka fara kiran magrub,
"Zan tafi ..." Inji ihsan cikin sanyin murya,
"Ki jira ya zo in rama maki marinki..." Inji Umma,
Dan girgiza mata kai tayi tana mikewa, itama Umma mikewa tayi
"To Dan Allah kiyi hakuri... Dan Allah kar ki fadawa mom dinki...banason wannan ya kawo matsala tsakanin mu...pls..." Tafada ahankali, kai ihsan ta gyada mata
"To Umma.. Bazan fada mata ba..." Rungume ta Umma tayi
"Nagode kinji... I will make sure bazai kara marin wata ba balle ke..." Kai kawai ta gyada mata tayi hanyan waje, rakota Umma tayi har compound Sannan ta koma ciki, tana bude gate ta fita Ayan na karasowa kallon ta yayi tare dayi mata gwalo,
"Azzalumi..." Tafada mashi, da sauri yayi kaman zai fita daga cikin motan aikam da gudu ta bar wajen ta kama hanyan gidansu.
Dariya yayi
"At least na koya maki respect da tsoro na...idiot... " horn yayi aka bude mashi gate, Umma tsayawa tayi bata ida shiga cikin falon ba. Parking lot ya nufa yayi parking Sannan ya fito ya nufi inda Umma take tsaye,
"Good evening..." Bai idaba ta kama mashi kunne tayi part dinshi dashi, lokacin Abba na fitowa daga nashi part din
"Lafiya dai ko?..." Inji Abba, kara kawai Ayan ke saki
"Laifi yayi..." Inji Umma, dariya Abba yayi yana cewa
"Kun fi kusa...amma kiyi saurin hukuncin don ya samu jam'i ..." Inji Abba.

Tana bude kofan part dinshi ta turashi ciki, kama inda Umma ta rike tayi yana shafa wurin, yana
"Wassshhh...Wallahi zafi Umma..." Umma rufe kofan tayi Sannan ta fara cewa
"Me yar mutane tayi maka ka mareta...." Zaro idanuwa yayi kaman baisan inda Umma ta dosa ba, Umma already ta gane abinda yake niyyan cewa, hannu Umma ta daga mashi
"Don't try me..." Ta fada mashi tana kara daure fuskanta,
"Umma wallahi kusan wata uku kenan kullum in ta ganni sai ta harareni tare da kirana Dan iska just because na rike mata hannu na kaudata daga kan titi...."
"Yo in ba iskanci ba ubanme yasa ka kama mata hannu?... Wallahi ka shiga hankalin ka...tunda nake nan ban taba samun sabani da kowa ba amma shine don rashin hankali zaka mari yarinyan da aurenta sauran sati two?..."
"Kam ashe gara dana ci kaniyanta data gama dani..." Yafada cikin ranshi, Umma tacigaba dacewa
"In ba don na bata hakuri ba iyayenta na iya daukan mataki kanka don rainin hankali ne marin ya mace...wallahi ka shiga hankalin ka..."
"Am sorry...." Inji shi
"Ba wani am sorry.. Kawai kaje kayi salla kadawo kaci abinci kaje gidansu ka bata hakuri..." Idanuwa Ayan ya zaro
"In bata hakuri bayan Wanda kika bata?..." Daguwa Umma tayi mashi
"In baka son ranka ya baci do as I said..."
"Ok Umma.. Amma basan gidansu ba...." Hararanshi Umma tayi
"You are not serious..."
"Wallahi Umma bansan takamemen gidansu ba nadaisan we're neighbors..."
Gida na biyar daga wannan gidan... " Umma ta amsa mashi Sannan ta fita. Da sauri ya daura alwallah ya fita sallah.


Ihsan na shiga falo ta hangi mom da siblings dinta zaune, itama zama zatayi
"Wai sai yanzu kika dawo daga rakiyan?..." Inji mom
"Eh sai yanzu tasamu adaidaita..." Tayiwa mom karya
"Ni wallahi na fara gajiya da zariyar wannan aminiyar taki...." Inji Janna kanwar ihsan, hararanta ihsan tayi
"Kar ki kara samun baki in inayin magana...." Inji ihsan
"La anty me ya samu fuskan ki...." Inji autansu Wanda suke kira da handsome
Hararan shi tayi batare data amsa mashi ba,
"Ku tashi kuje kuyi salla h..." Inji mom da nake tunanin ba cikin yanayin salla take ba, dukkan su mikewa sukayi tare da haye upstairs, bayan kaman minti biyar sai ga ihsan ta sauko mom dake zaune falo har lokacin kallon ta tayi
"Nace go and pray...." Mom ta fada cikin fada,
"Mom nayi...." Idanuwa mom ta zaro
"Kinyi me?..."
"Sallah mommy...." Kallon haushi mom ta tsaya yi mata
"Wato ihsan har yanzu baki jin magana ta ko?.... Bana hanaki 3 minutes prayer ba?..…ke kullum in few seconds kin idar da sallah despite all the problems surrounding you.... Ke da zaki zama uwa watarana in baki saba da prayers ba me zaki yiwa yaranki...."
"Wallahi... Nayi"
"Keep quite...kinyi din ubanki?...wani irin prayer zakiyi in 3 minutes... Why bazaki nutsu ki fadawa Allah problems dinki ba...."
"AI mom bani da wata matsala...."
"Wannan yarinyan sakara ce...siblings din problems garesu da suke praying?... Look har yanzu basu sauko ba...to wallahi ki shiga hankalin ki..." 1
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💚💙💜🖤❤💛
KAWARTA CE SANADI
💜💛💚🖤❤💙


®zuwairat( ummu Maryam)6⃣Haka mom ta tisa ta gaba ta dinga yi mata fada kan rashin maida hankali kan aduoi tunda shine takobin mumini ihsan kam gani take bata da wata babban matsalan da zai bukaci ta kwana kan praying mat, da matsalan ta shine yanda ake fasa aurenta Kuma yanzu alhamdulillah gashi aurenta sauran sati two, batasan neman zabin Allah at all times is very important ba.


Tare Ayan da Abba suka dawo daga masjid, Abba wucewa yayi part dinshi shima ya wuce nashi karamin part, direct bathroom ya shiga yayi wanka ya fito Sannan ya saka light english wears wato black three quarters da white t-shirts.
Main part ya je ya tarda Umma da Ismail tare da Nafisat wato antymu,
"Yaya what keep you long.... Tun dazun nake jiranka kazo in baka abinci..." Antymu ta fada kaman ita ta haifeshi kasancewan ita ke feeding dinshi, kunnuwanshi ya kama
"Sorry for keeping you waiting..." Yafada Sannan ya gaida Umma ta amsa tana hararanshi, kan dinning ya nufa antymu ta mike ta bi bayanshi, zama yayi itakuma tayi serving dinshi Sannan ta fara feeding dinshi yana ci yana yayi kasa2 da murya Sannan ya fara cewa
"Antymu kisan yarinyan nan da nake baki labarin tana zagina?..." Ya tambayeta yana bude baki tana juye mashi abinci a baki, kai ta daga tare dacewa
"Eh yaya... "
"Yau na mareta...." Bai idaba ta saki murna wai taji dadi da yayanta ya mari wacce take zagin shi
"Yauwa....haka nake so...kaga bazata kara zaginka ba...." Tafada tana mai jindadin abinda yayanta yayi
"Har kuka tayi...." Ya fada Sannan ya fara magana irin na ihsan yana cewa
" _Allah ya isa_ ...INA kara daga hannu tayi saurin durkusawa...." Dariya tayi sosai har Umma ta kallesu, tana mamakin irin shakuwan dake tsakanin abubakar da Nafisat har tunani take yanda zai kasance ranar da yayi aure ya bar gidan
"To uwayen kilibibi...kayi sauri ka tafi inda nace...." Inji Umma, karaf Nafisat tace
"Ai Umma bai koshiba tukunna... Duka spoons shabiyar yaci Kuma akalla yanacin spoon ashirin da biyu zuwa da uku...." Dariya ne ya kufce wa Ayan
"Wato kina counting spoons din abincin da nake ci?..." Da sauri tace
"Eh mana...har tuwo nasan loma nawa kakeci ka koshi..." Umma ma dariya tayi
"Kin yi ki gama...nan da 1 to 2 years aure zaiyi ya bar gidan nan.. Sai inga ta kirga loma ko spoons..." Inji Umma, marairace fuskan antymu tayi da sauri Ayan yace
"Antyna kwantar da hankalin ki...ko nayi aure tare dake zan tafi in su Umma sunki saidai in fasa auren...."
"Kayi sauri ka gama cin wannan abincin kazo ka wuce ko Kuma in fadawa Abbanku abinda kayi...." Tafada afusace
Kallon shi antymu tayi Sannan tace
"Yaya wai ina zakane?...", Dan kara sauke muryan shi yayi yanda babu Wanda zaiji abinda zaice Sannan yace
" wai gidan yarinyan Umma tace inje in bata hakuri... "
"Cikin wannan Daren?...ko gidansu babu nisa?..." Ta jero mashi questions cikin whisper wai don kar aji hiransu,
"Ba nisa...nan neighborhood ne..." Shima ya amsa mata cikin whisper, idanuwa ta zaro
"Wacece?..." Ta tambayeshi with anxiety
"Baki santaba..."
"Ai nasan yanmatan street dinmu duka..."
"Nidai feed me in tashi ishai prayer na gabatowa..." Dan bata fuska tayi
"To shikenan tunda you are keeping secrets from me amma remember you said no secret..." Tafada kaman wata mate dinshi. Banza yayi daita yacigaba da amsan abinci daga hannun ta har ya koshi ya mike ya koma falo ya zauna kusa da Umma, hararanshi tayi
"Ka tafi mana..kodai sai na fadawa abbanku zakaje?../"
"Wallahi Umma zanje amma bari abincin danaci yayi digesting...sai inyi sallah Sannan inje...,"
"Kai kar ka raina min wayau....maza tashi!" Umma ta daka mashi tsawa ba don yasoba ya mike ya bar falon.
Waje ya fita ya karewa quite street din ido Sannan ya fara takawa ahankali yana tafiya yana counting numbers na gidaje, a gida na biyar after nasu ya tsaya still hannuwanshi cikin aljihunshi, tsaya kallon gate din yayi yana cewa
"Allah yasa baki da rabon shan wani marin da wannan Daren cos I won't tolerate any act of stupidity..." Yafadawa kanshi, kara kallon gate din yayi har lokacin hands dinshi cikin aljihunshi, kaman ya koma gida yayiwa Umma karya yake ji amma he knows his mother too well, yasan she will definitely ask her, hannun shi na hagu ya fiddo daga cikin aljihunshi ya taka zuwa bakin gate din, ahankali ya saka hannunshi ya danyi knocking , shuru yaji babu alaman zaa bude gate din, kara knocking yayi wannan Karin da karfi, karamin kofan aka bude yaga wani tsohon mutum da gani mai gadinsu ne, dayan hannuwanshi ya fiddo yayi tare dayiwa tsohon sallama gaisawa sukayi Sannan Ayan yace
"Baba Dan Allah yarinyan gidan nan nakeson gani..." Yafada cikin natsuwa,
"To wace daga cikin su?..."Tsohon ya tambayeshi,
" wata fara mai manyan idanuwa..." Yafada yana mamakin yanda akayi ya Iya bada kwatancenta, dariya tsohon yayi
"Hajiya ihsan kenan..." Inji tsohon, Ayan kauda kanshi gefe yayi tare da dan tabe baki, tsohon juyawa yayi batare daya rufe gate din ba, Ayan dan leka cikin compound din yayi, gidan nada kyau da girma amma ko kadan bai kai nasu girma da kyau ba, komawa baya yayi ya maida hannuwanshi cikin aljihunshi.

Alokacin duk su ihsan na zaune a falo banda dad dake abuja, duk ahankalinsu na kan movie da akeyi a zee cinema, baba ne yayi sallama ya shiga falon, dukkan su maida hankalin su
Sukayi kanshi, gaida Hajiya yayi ta amsa da sakin fuska kaman yanda ta saba, tsohon kallon ihsan yayi Sannan yace
"Hajiya karama kizo kinyi bako...." Ihsan kallon shi tayi Sannan tace
"Ni?..." Ta tambayeshi sounding surprised don tasan Mahmoud bai kara zuwa yau
"Eh...hajiyata..." Inji baba maigadi. Dariya Janna tayi tana cewa
"Ko ma waye baisan aurenki sauran two weeks bako?..." Hararanta ihsan tayi
"Baba ko zaka tambayo waye?..." Ihsan ta fada mashi don ko kadan batason missing movies din.
"Baban zai tambayo maki?...come on kije ki dubo da kanki.." Mom ta daka mata tsawa, da sauri ta mike har lokacin tana sanye da doguwar rigan shadda, kanta ba dankwali, upstairs ta tafi sai turo baki take, da sauri ta dauko Vail kawai ta yafa Sannan ta fito duk haushi ya isheta.

Ayan komawa yayi daga gefe ya maida hannuwanshi cikin aljihunshi ya tsaya batare daya shiga cikin gidan ba, tsohon ne ya dawo ya shaida mashi tana zuwa.

Few min later yaji kafan takalmi, Dan kara lekawa yayi ya gan ta taho, da sauri ya koma ya tsaya fuskan shi dauke da murmushin mugun ta,
Ihsan tsayawa kalle2 tayi taga ba kowa,
"Baba yana ina?..." Ta tambayi baba maigadi
"Yana kofar gida...." Ya amsa mata, Dan bata fuska tayi
"Ka fada mashi ya shigo mana..." Tafada tana gyara tsayuwanta, duk Ayan najin abinda
Take cewa, kara gyara tsayawan shi yayi, da sauri baba maigadi ya leko da kai
"Dan samari ka shigo ciki...." Yafadawa Ayan, Ayan daga kanshi yayi ya kalleshi Sannan yace
"Tazo sauri nake sako zan bata...." Yafada cikin whisper don kada ihsan data kafa kunne don jin muryan mai magana taji abinda ya fada mashi. Nan ya koma ya fada mata abinda yace, kallon bakin gate din tayi Sannan ta tako ahankali zuwa bakin gate, daidai bakin gate ta tsaya ta Dan leka dakanta karaf sukayi ido hudu dashi, fuskan shi kaman bai taba dariya ba amma sai da ya daga mata gira daya, tana ganin shi ne tayi mashi wani irin dirty and disgusting look tare dacewa
"Mtssssssssss...." Don tafi seconds goma tana Jan tsokin Sannan tajuya da niyyan komawa ciki, da sauri ya fixgota waje tare da rufe mata baki don ba karamin ihu taso yi ba,
"Wa kike yiwa tsoki?..." Ya tambayeta, dukan shi ta farayi don yanda ya rike mata waist har cikin pelvic dinta take jin hannun shi, gashi babu bakin ihu,
Kara jawota yayi daf dashi yayi saurin rufe gate da dayan hannun shi Sannan ya Kara danne bakinta yakara cewa
"Wa kike yiwa tsoki?..." Ya kara tambayan ta yana zaro mata idanuwa, hawaye tafarayi don ko numfashi da kyar takeyi,
"Kin raina ni ko?..." Ya tambayeta yana kara danne bakinta da karfi, da sauri ta girgiza mashi kai tana hawaye,
"Zan saki bakinki yanzu amma kika sake kikayi min ihu sai na cire maki hakora...nod if you understand..." Da sauri ta yi nodding kaman agama lizard, idanuwanta data gwalalo ya kalla for few seconds Sannan ya cire hannuwanshi daga jikinta, da sauri tayi niyyan komawa ciki ya kara chafko ta, tsayawa tayi har lokacin bata bar hawaye ba
"Dan Allah kayi hakuri... Bazan kara zaginka..." Tafada tana kuka
"Good.. Daman abinda nakeson ji kenan... Yanzu nazo nan ko ban zoba?..." Ya tambayeta sounding very serious
"Kazo..." Tafada tsoro na ratsata, don street dinsu da ba kowa, ihunka banza kuruwanka wofi,
"Dan Allah kayi hakuri zan tafi...."
"Kifi ruwa gudu..." Yafada yana juyawa da niyyan tafiya, da sauri ta shiga cikin gida Sannan ta tsaya bakin gate ta kalle bayan shi ta fara cewa
"Allah yaisa mugu azzalumi... Ban yafeba...dan iska kawai Kuma ka Sani Wallahi tallahi ba tsoron ka nake...mugu... " tafada tana feeling confident saboda tana tsaye cikin gidansu, juyawa yayi ya kalleta ya saki murmushin takaici yana cewa
"Ki fito mana..." Bai idaba ta katseshi dacewa
"Ban fitowa.. Mugu..." Da matsawa kusa da gate din yayi ta jabaya da sauri, dariya yayi Sannan yace
"Ko ranar auranki na kamaki sai naci ubanki... That is not a threat but a promise..."
"Har ka isa?... To wallahi ka bar ganin ka mareni dazun na kyale ka...to wallahi ka Kara gigin tabani sai court ta rabamu...." Dariya ya karayi
"To ki fito mana sai court din ta rabamu?..."tsoki kawai taja tare da barin gurin har lokacin gate din na bude, bayan ta Ayan yabi da kallo yayi kwafa Sannan ya tafi.

Ihsan na shiga falo bata tsaya kallon ba ta haye upstairs da gudu don batason karyan alkawarin data dauka da babu abinda zai hanata fadawa mom irin cin mutuncin da Ayan yake yi mata.

Da sauri ta dauki wayanta tayi dailing number husna, daga chan bangaren saida husna taja wani irin tsokin haushi da tsana don tunda ta dawo take jin haushin abinda ya faru tsakanin Ayan da ihsan, ita ba Marin da Ayan yayiwa ihsan ke damunta ba sai hannun Ayan daya taba fuskan ihsan, wani irin kishi kawai takeji yanzu ji take kaman ta jawo ranar auren Mahmoud da ihsan cos she really want ihsan out of the picture.
"Babe ya kike?..ya fuskan ki hope bai tashi ba...."" Husna ta tambayeta sounding very caring, cikin kuka ihsan tafara cewa
"Babe duk Marin da wannan Mara mutunci yayi min bai isheshi ba sai da yazo har gidanmu..." Bata idaba husna ta mike zaune kasancewan kwance take tare da katseta dacewa
"What!... Me yazoyi!..." Tafada cike da kishi, ita ihsan was thinking is out of love, cikin kuka ihsan tacigaba dacewa
"Babe har kamamin waist...." Bata idaba husna ta fashe da wani masanacin kuka,
"Allah ka kawo sati two..." Ta fada tana kuka sosai don gani take kilan Ayan son ihsan yake,
"Why did you say that?..." Ihsan ta tambayeta tana mamakin jin irin kukan da husna takeyi wani irin madacine ke fita daga cikin muryan ta
"Don kiyi aure...kafin wani abu ya faru tsakanin ki da shi...." Tafada tana kuka hannun ta daya dafe da kirjinta don ji take kaman heart dinta zai fito waje. Ihsan zata bude baki tayi magana husna tayi saurin cewa
"Babe my battery is about to die...we will see tomorrow..." Bata jira amsanta ba ta kashe wayata. Bige kanta ta dingayi da kasa don imagining abinda ya faru tsakanin Ayan da ihsan kawai
"Me he have kiss her with his lovely lips... No...no...no...wallahi you are mine...Wallahi duk wacce tayi kokarin rabani da kai sai ya bakunci lahira cos I can't let you go..."
Aranan batayi baccin kirki ba don kuka kawai ta kwanayi.

The following day tazo gidan su ihsan kaman babu abinda ke cikin ranta, nan ihsan ta fada mata duk abinda ya faru tsakanin ta dashi amma abinka da munafuka gani take there is more to the story.

Datazo tafiya bakin gate kawai ihsan ta rakata don ko kadan bata fatan ta kara haduwa da Ayan kafin aurenta.

Bayan kwana uku da faruwan hakan Ayan bai kara ganin ihsan ba Kuma bai damu ba don yasan har da tsoron shi ya hanata fitowa cos at times yana ganin husna ita kadai that is duk ranar da Allah yasa ya dan kalleta don even for a second bazai Iya bada description dintaba cos he don't care about her.

Kullum husna sai tazo gidan su amma ihsan bata raka waje iyakanta bakin gate.

Ayau datazo tafiya ta hangi motan Ayan
"I have to talk to you today...." Ta fadawa kanta, tana tafiya ahankali, tana zuwa daidai saitin motan shi ta dan daga mashi hannu alaman wait.
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💙💚💜🖤💛❤
KAWARTA CE SANADI
💛❤💚🖤💙💜


®zuwairat( ummu Maryam)


7⃣Ayan dake tuki ahankali ya ga kaman ta daga mashi hannu ya tsaya amma dayake Dan duniya ne sai yayi kaman bai ganta ba, kara waving dinshi tayi yana kallonta ta wutsiyan ido amma still bai daga kai ba har yazo zai wuce ta yaji tace
"Pls excuse me..." Ta fada da karfi, bai kalleta ba ya Danyi parking gefen titi, husna jikinta sai rawa yake ta tsallaka to the other side, har lokacin Ayan bai daga kai ba saida tazo wurin bakin kofan motan Sannan tace
"Good evening..." Ta fada muryan ta na rawa, daga kai yayi ya kalleta don yaji yanda muryan ta ke cracking,
"Lafiya..." Ya amsa yana kallon gabanshi, ahankali tafara cewa
"Daman inason yi maka magana ne...." Ayan Dan tabe bakin yayi Sannan ya fara juye2
"Are you talking to me?..." Ya tambayeta, ahankali ta gyada mashi kai,
"What?..." Ya tambayeta, husna wani irin dadi takeji cikin ranta wai gata ga Ayan wuri daya, ita batason yanda muryan ta ke rawa amma she couldn't control it, don har jikinta shaking take batasan haka tsayawa kusa da masoyi yake ba.
"Daman its about my friend..." Ta fada mashi still muryan ta na rawa, daga kai yayi ya kalleta
"Wai why is your voice cracking?.." Ya tambayeta babu wasa cikin tune dinshi, murmushin karfin hali tayi don kafafunta sai rawa suke,
"Bakomai..." Ta fada cikin sanyin murya.
"Then why do you stop me...." Ya tambayeta, ta cigaba dacewa
"Daman I want to ask you to pardon my friends lack of manners...." Bata idaba Ayan ya chanza fuska tare dacewa
"Aiko ko tayi?..." Da sauri ta girgiza mata kai
"Aa...I just...."
"Please don't waste my time... Ita ta aikoki ko ke kika aiko kanki?...." Ya fada yana kokarin calming temper dinshi,
"Ba ita ta aikoni....." Bata idaba ya kara katseta dacewa
"Then why do you stop me?..." Ya fada cikin fada,
"Ba komai...."
"Ke dalla rufemin baki...wato kun maidani topic of discussion dinku ko?...in ba don gulma da iyayiba name zaki tsaida ni ?...do I look like your mate?..." Ya daka mata tsawa, husna sunkuyar da kai tayi tare da girgiza mashi kai Kuma abinda ke bata mamaki shine ko hannu zai daga ya bigeta bazata ji haushin shi ko kadan ba har in short she loves the way he nags.
"Kayi hakuri da rashin respect din kawata...."
"Keep quite... Ai da gani both of you a birds of the same feathers so you flug together...." Murmushi tayi
"Ba halin mu da..." Bata idaba ya kara katseta dacewa
"I don't bloody care...both of you can go to hell of all eternity...." Yafada cikin fada sosai
"To ka yafe mata..."
"You people should stay far away from me...Kuma ki fadawa wannan yarinyan ban fidda ran zan kamataba...if she likes she should run to China sai ranar da aka daura auranta ta tsira daga hannu na...and you don't ever stop me again...." Yana kaiwa nan ya tada motanshi,
"We're sorry..." Tafada mashi amma bai saurareta ba yayi gaba abun shi,
Ayan dai irin mutanen nan ne marasa daukan rainin hankali, ya iya wasa da dariya amma even he's friends knows better, ko are hospital da kyar ayi patients da basu San halin shi ba, that is Mr fabulous kaman yanda friends dinshi suke kiranshi Sannan wasu na kiranshi da black diamond amma Sam bayason wannan sunan cos most of the time suna amfani da wannan sunan don bata mashi rai especially Yusuf da mohd.

Yanzu sauran sati daya bikin ihsan, duk hankalin family dinsu kwance tunda duk cikin ranakun aurenta babu Wanda yake kaiwa haka kafin abun ya tarwatse, husna kam yau ta dawo gidan su ihsan da zama wai har sai an gama biki zata koma gidansu, son Ayan kam kaman zai kasheta Kuma ko da wasa ba taba fadawa ihsan ba don cikin ta yafi rijiya zurfi, saidai yau natazo ihsan taga ramanta sosai sabanin jiya Kuma ba komai ya haddasa hakan ba sai rashin bacci don yau kwana tayi zaune saboda mafarkin datayi wai ihsan ta kwace mata flowern da take mutu kar so, dukda batasan maanar mafarkin ba amma tasan is not something good, aduan ta kawai Allah yasa ayi bikin ihsan lafiya Sannan tasan abinyi kan Ayan.
"Babe wai meke damunki ne kika koma haka?..." Ihsan ra tambayeta,
"Ya na koma?..." Itama ta tambayeta
"Wallahi babe naga kaman idanuwanki sun koma ciki...ko da abinda ke damunki?...ko dayake hardly kiyi sharing problem dinki dani amma ni komai nawa kin sani...." Bata idaba husna ta balla mata harara
"Yanzu kina nufin bani sharing problems dina dake?..."
"Yo eh mana...."
"Kam amma kin Iya batawa mutane rai wallahi...to ba komai yasani raman nan ba sai missing dinki...wallahi kullum dake nake kwana nake tashi,...yanzu in kun tafi abroad saidai a waya..." Raurau ihsan tayi da man idanuwa cos yanda husna tayi maganan babu mai cewa she's lying
"But babe ai ba mutuwa bace...nima wallahi Allah kadai yasan yanda nakeji muna tare for the past 18 years amma aure zai rabamu...." Ihsan tafada tana fashewa da kuka, husna tabe baki tayi Sannan ta taso ta rungume ta suka fara kuka kaman wayanda akayiwa mutuwa, ita ihsan tana kukan rabuwa da family da kawarta ita kuma husna tana kukan son Ayan da take da baisan da zamanta ba, haka suka sha kukansu su kadai cikin bedroom din ihsan Sannan suka sauko don taya mai aiki hada kayan dinner, mom na zaune falo su Kuma suka wuce kitchen, wayan ihsan ne ya fara ringing murmushi tayi kasancewan tasan mai kiranta, picking tayi suka fara soyewansu,
"Babyna zan tafi Kaduna yanzu..." Inji Mahmoud, da sauri ihsan tace
"Da yamman nan zaka kd?...Dan Allah ka bari sai gobe...." Tafada kaman zatayi mashi
Kuka,
"Don't worry insha Allah gobe da wuri zan dawo..."
"Yanzu fa after four...dare zaiyi kafin ka isa..." Tafada mashi cikin shagwaba, husna sai kallon ta take tana fere doyan sakwara,
"Kiyi hakuri in tafi...is important...is urgent..." Yafada mata ahankali,
"To shikenan.. Drive carefully..." Tafada cikin sanyin murya. Hira suka danyi Sannan sukayi sallama.

Around 6:00 sun gama komai suka j
Jera abinci kan dinning,
"Babe wallahi jikina ba dadi...am feeling feverish..." Ta fada tana ajiye ruwan wanke hannu kan dinning,
"Kin ma raina mana wayau....salon kice baki cin abinci ko?...wallahi baki isaba...." Inji husna,
"No babe...kawai jikinna has suddenly becomes cool...Kuma wallahi tundazun lafiya ta lau...sanyine ya dan kamani yanzu..." Inji ihsan da duk jikinta yayi sanyi for no reason,
"Sorry... Muje muyi wanka kilan gajiyan daka sakwara ne...let's go and shower kafin su mom su sauko...." Inji husna. Daidai stairs suka ci karo da mom dake sauko tare da handsome sai mai bima Janna maisuna Aisha,
"Ina zaku Kuma?..." Ta tambayesu,
"Wanka zamuyi..." Ihsan ta amsata,
"Kuyi sauri kufito kuci abinci kafin magrub..." Inji mom. Mom na saukowa anty Zuwairat tare da wata sister mom suka shigo, sai baba mai gadi daya fara shigowa da wasu foreign bedsheets cikin kwalin su. Mom rungume yarta tayi tana cewa
"Ai anty wannan hidiman is too much..." Anty Zuwairat banza tayi daita ta zauna kan daya daga cikin kujeran falon, baba maigadi kara komawa yayi ya shigo da wasu kayan, atakaice saida yayi kusan taki biyar yana shigo da kaya kala2, mom kam baki ta bude, don kayan are far beyond her expectations,
"Wannan shine kayan da aka saya da kudin da family suka tara..." Inji anty Zuwairat,
"Nagode..." Kawai mom ta dinga maimaitawa,
"Ina sauran yaran?..." Ta sake tambayan ta
"Suna upstairs...." Mom ta amsa mata. Hira suka dan yi kafin dad ya shigo falon, gaisawa sukayi dasu anty Zuwairat Sannan suka hau kan dinning. Tare ihsan da Husna abinci suka ci, suna gamawa ana kiran magrub, dad da handsome suka tafi masjid, dukkan su watsewa sukayi donyi salla, bayan kowacce tayi suka dawo falo, banda mom da su anty da suke dakinta suna magana.

Suna saukowa wayan ihsan ya fara ringing, jin mai kira yasata sakin murmushi tare dacewa
"The person I need..." Tafada kasan makoshinta Sannan tayi picking tare dayi sallama, daga chan bangaren aka amsa, muryan datajine yasata kara daga wayan daga kunnenta don tabbatar in da Mahmoud take magana, confirm number dinshi ne amma ba muryan shi ba
"Pls waye... Pls give the phone to the owner..." Tafada cikin sanyin murya, daga chan bangaren akace
"Dan Allah kece matar mai wannan number?.." Mutumin ya tambayeta,
"Tofah..." Ihsan ta fada Wanda hakan yasa dukkan su suka maida hankalin su kanta including husna,
"Eh nice waye Dan Allah?...." Tafada gabanta na faduwa Wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.
Daga chan bangaren aka ce
"Daman mai wannan number ne suka samu accident... Kuma Allah yayi masa cikawa...." Da sauri ihsan ta daga wayan daga kunnenta, tare da sakin murmushi, Kara maidawa tayi kunnenta Sannan tace
"Pls haram ne tsorata Muslim... Pls this is not funny...."
"No...daman number dayayi saving da mom is not going through dats why muka kira da number dayayi saving da my queen...so pls in har kin san mai number pls ki shaidawa family..." Bai idaba ta wurgar da wayan tare dacewa
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun.!!!!.." Tafada da karfi, Sannan ta yanke, daman tunda su husna na Janna sukaji irin wayanda takeyi suka maida hankalin su kanta, tana wurgar da wayan sukayi kanta amma kafin sukai har ta sume, da gudu husna, Janna da Zainab suka karaso wajenta suna kiranta da karfi tare ihu Wanda yasa mom sa su anty Zuwairat saukowa da gudu, husna sai girgiza ihsan take amma ko motsawa batayi,
"Me ya faru!..." Mom ta tambayesu cikin tashin hankali,
"Wani ne ya kirata da number yaya Mahmoud shine...." Kuka ne yaci karfin Janna tayi shuru, da gudu anty Zuwairat ta amsheta daga hannun husna tafara girgiza ta tana kiranta amma shuru, mom cikin tashin hankali ta amshi wayan ihsan daga hannun Janna tayi dailing number Mahmoud nan aka shaida mata abinda ke faruwa, kuka tafarayi tana salati,
"Wai meke faruwa ne!..." Anty zuwairat ta tambayi mom
"Anty mahmoud ya rasu...." Nan falon gabaki daya aka fara kuka, da sauri mom tayi dailing number dad.

Alokacin dad da Abba su Ayan tare da Ayan da handsome sai superman suna dawowa daga masjid cos most of the time tare suke dawowa, dad da Abba na gaba sai Ayan da sauran yara na bayan su, wayan dad dake cikin aljihunshi ne yafara vibrating, fiddowa yayi ya duba yaga ihsan, da bazai dauka ba amma sai ya tuna bata taba kiranshi haka na so picking yayi, cikin kuka mom tafara cewa
"Alh dan Allah ka taho a tafi da ihsan hospital.. Mahmoud ne ya rasu..gata nan ko motsawa batayi..." Tafadi magana kaman batasan abinda take fadaba don kawai hakan maganan suka dinga fitowa daga bakinta
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!..." Da dad ya fada ya maida hankalin su Abba kanshi,
"Lafiya dai ko?..." Abba ya tambayeshi,
"Suitor din yarinyan nan ne Allah yayiwa rasuwa...yanzu ance she's in a bad shape..." Dad ya amsa mashi yana sauri sosai, Ayan kallon dad yayi amma baice kala ba,
"Subhanallahi!..." Inji Abba
"Bari in yi sauri in kaita hospital..." Inji dad, da sauri Abba ya kalli Ayan Sannan yace
"Son kabi shi..if her condition is critical call ambulance..."
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💙❤💚🖤💜💛
KAWARTA CE SANADI
♥💜💛🖤💚💙


®zuwairat( ummu Maryam)


9⃣Da sauri ya dinga cin abincin dukda baisan inda abinci ke tafiyaba. Ko rabi baiciba ya mike, ya koma falo, Umma kallon shi tayi surprisingly Sannan tace
"Son har ka koshi?...ko dan yau antymu batayi feeding dinka ba?..." Ta tambayeshi
"Umma na koshi...inason in je in duba drip din kar ruwan ya kare..."
"Ok...ya condition dinta hope is not bad..." Kai ya girgiza mata
"Kawai shock ne..she will come around..." Yafada mata.
"Ok...sai gobe ni zanshiga...."
"To Umma... Bari in tafi chan..." Tafada yana barin falon.
Part dinshi ya tafi yayi shower sai sauri yake kaman ance be early or be dead, fitowa yayi daure da towel, da sauri ya bude wardrobe ya dauko Jordan baki da blue polo, turare ya fesa Dan tsayawa yayi yana cewa
"What am I doing this for?..." Ya tambayi kanshi, sakin murmushi yayi Sannan yace
"Am always use to looking good... So is not because of anybody...." Daure fuska yayi
"Who say it is because of somebody?..." Ya tambayi kanshi, dariya yayi ya fita tare da jawo kofan.

Bakin gate yaje ya kira security dinsu
" zan fita yanzu Kuma kika sai dare sosai zan dawo...so pls kar Ku barni inyita knocking... " ya fada mashi
"To shikenan..." Mutumin ya amsa mashi Sannan yafita, da sauri ya isa gidansu ihsan yayi knocking baba maigadi ya bude mashi ya shiga, sallama yayi dad da mom suka amsa mashi, shiga yayi ahankali amma ya rasa courage din hawan sama,
"Har ka dawo?..." Dad ya tambayeshi,
"Eh..daman don Karin ruwan ya kare ..." Ya amsa mashi kanshi kasa.
"Ok...ka hau saman mana...." Dad ya fada mashi. Bai Kara cewa kalaba ya hau sama.

Da sallama ya shiga har lokacin hannun ta cikin na anty, husna na zaune kan kujeran dressing mirror sai handsome da Janna na zauna kan gado kusa da ihsan, yana shiga husna ta mike,
"Ka zauna nan..." Banza yayi daita ya kalli ruwan da ko rabi bai kaiba, hannun ta ya kama don ganin in ruwa na zubowa normal, sai da ya gama inspecting hannun Sannan ya koma gefe yana kallon swollen lips dinta, kallon ta ya tsaya yi kaman madubi,
"Wannan guy da ya rasu ya mutu da bakin cikin rashin samunki amatsayin matarshi..." Yafada cikin ranshi.
"Ka zauna mana...." Anty ta fada mashi tana nuna inda husna ta tashi. Zama yayi ya fiddo wayanshi ya fara lase2, husna kam kallon shi kawai take amma ko side dinta bai kallaba balle yaga irin kallon da takeyi mashi, Janna dai ta gani Kuma tana mamakin irin kallon da take yi mashi.
Around 9:30 anty ta kori Janna da handsome suje su kwanta sai lokacin mom ta shigo tare da dad,
"Ko zaka nuna mana yanda zamu cire ya n drip din ya kare tunda time is going Kuma gobe zaka aiki..." Dad ya fadawa Ayan,
"No problem.. Zan zauna ya kare sai in tafi..." Ya amsa mashi cikin natsuwa.
Suma zama sukayi for almost an hour Sannan dad ya tafi ya kwanta har lokacin drip bai kareba, anty ce ta umarci mom ta je ta kwanta dukda bataso amma batason tayiwa yarta gardama,mikewa tayi tare dayiwa Ayan godiya tafita,
"Anty kije ki kwanta zan kula daita...." Inji husna dake son dakin ya rage daga ita sai Ayan,
"Don't worry..." Kawai anty tace mata.
Motsi ihsan tayi Wanda yasa Ayan mikewa ya dawo kusa daita, bude ido tayi, bata gani sosai don komai double take gani,
"Zan shiga....bathroom...." Ta fada,
"Ta yaya zaki shiga bathroom ga drip hannun ki?..." Anty ta fada, fuska tayi kaman zatayi kuka,
"Bari in cire mata in ta dawo sai in maida mata tunda ya kusa karewa..." Inji Ayan, ihsan Kara bude idanuwanta data lumshe tayi ta galla mashi harara, hannun ta ya kama ya cire drip. Mikewa tayi kokarin yi juwa ya dauketa da sauri Ayan ya riketa kafin anty da husna su kai gareta, kwace kanta tayi husna jitake kaman kirjinta zai fito don ba karamin haushin abinda ke faruwa takeyi ba amma she don't have a say.

Tana dawowa ta kwanta tana cewa
"Yaya Mahmoud...." Tafada tana rufe idanuwanta nan bacci ya dauketa.

Sai wajen 11:30 drip din ya kare Ayan ya cire mata yayi masu sai dasafe ya tafi.

The following day gidan su ihsan ya cika da yn jaje wasu sai gulma suke suna cewa da gani wannan yarinyan miyagun aljanu gareta Wanda basuson tayi aure.

Tare da Abba da dad da wasu family akayi janaizan Mahmoud cos an maidoshi Kano.

Kukan ihsan kam ba kadan ba don duk yanda su anty da sauran dangi ke kokarin hanata abun cin tura yayi.

Ayan bai tashi da wuri ba koda ya tashi da gudu ya shiga wanka ya shirya cikin manyan kaya, ya tafi office bayan yayiwa Umma sallama.

Yanayin shi ya nuna yana cikin jin dadi don fuskan shi fayau kallon shi Mohd da Yusuf sukayi Sannan Mohd yace
"Fab yadai?..." Kallon shi Ayan yayi
"Ban gane yadai ba?...." Shima ya tambayeshi
"Ai munga you look happy... Ko yar mutane ka kara Mari?..." Yusuf yafada. Dariya Ayan yayi
"Not at all... Wannan yafi mari...wannan yarinyan suitor din ya rasu jiya...."
"Ayya...." Su Mohd da Yusuf suka fada in chorus, kallon haushi yayi masu tare da tabe baki Sannan yacigaba dacewa
"So she was having a little bit of nervous breakdown... So unluckily for her sai Abba yasa in je in dubata..." Dariya mugun ta yayi Sannan yacigaba dacewa
"Yanzu allura 20 zanyi mata 2 everyday for ten days..." Idanuwa suka zaro
"Allura 20 for nervous breakdown?..." Yusuf ya tambayeshi, dariya yayi
"No...na zagina ne...." Ya amsa mashi with I don't care tune
"Amma gaskiya you are wicked..." Inji Yusuf
"Ashe wicked... Ai da farko danaje I want to pity her amma sai na lura conditions din data shiga bai sa tayi taushi ba...so zan da koya mata hankali ne..."
"What if something happens to her in the process?...." Mohd ta tambayeshi
"Nothing will happen... Kawai paracetamol ne da gentamacin...."
" amma kasan too much of paracetamol is dangerous to the liver ko?..." Inji Yusuf, hararanshi Ayan yayi
"To the professional doctor ka koya min tunda kafini experience..."
"Wallahi babu wani zancen experience.. Kawai mugun ta zakayi...banza black dai..." Bai idaba Ayan ya wulla mashi wani decor dake kan table din gaban shi, da sauri Yusuf ya kauce, su biyu mikewa sukayi shima Ayan ya mike, da sauri suka kai bakin kofa
"Banza wande coal..." Inji Yusuf daya fita da gudu yana dariya, shima Mohd cewa yayi
"Sai shegen gardama kaman arnan farko...idiot black diamond... Ga bakin fuska ga bakin halin...." Kafin Ayan ya karaso inda yake har ya bar wurin da gudu, curridor Ayan ya biyosu yana cewa
"In banyi suspending dinku ba Ku kirani da shege...." Bai idaba Yusuf daya kusa fita daga curridor yace
"Daman AI shegen ne kai...black diamond kawai...." Ayan tsayawa yayi ya rike kugunshi yana jin inama yarane su Mohd da babu abinda zai hanashi dukansu, kwafa kawai yayi ya koma cikin office
Sai daf da magrub ya dawo gida, wanka yayi ya shiga falo antymu tayi feeding dinshi as usual Sannan ya koma falo kusa da Umma dake zaune,
"Zan tafi masjid daga nan zan wuce Chan gidan inyi mata injections..." Inji Ayan
"Ok son...amma gaskiya ina tausayawa yarinyan nan...dazun danaje ta koma kaman ba ita ba..." Ayan kauda kanshi yayi gefe ya tabe baki Sannan yace
"Kyaleta Umma.. Rashin danganane...." Yafada yana mikewa, fita yayi yana rike da hannun Ismail, bakin gate suka tadda Abba suka wuce masjid bayan shi sa Ismail sun daura alwallah nan waje.

Tare da dad suka dawo gidansu ihsan lokacin few women ne zaune falo, izini dad yayi mashi ya tafi upstairs.

Ihsan na zaune kan praying mat sanye take da long hijab, idanuwanta sunyi mugun kunburi, wasu yanmata su biyar ne zaune cikin dakin Cikin su har aminiyarta husna da ganin sauran yanmatan cousins dinta ne. Ihsan ta kurawa selfie dasukayi da Mahmoud ido, dukkan su dariya suke ya sanda ya daukesu. Wasu sabon tears ne suka kara gangaro mata, sallama Ayan yayi ya shiga dakin, ahankali ta daga kanta ta kalleshi da swollen eyes dinta, kuka ta farayi tana cewa
"Banason allura,... Dan Allah kar kayimin allura..." Duk yanmatan dake dakin dariya sukayi farayi banda husna datayi mutuwan zaune don ganin heart desire dinta,, daya cewa tayi
"Wallahi sis da abun dariya kike...allura kikewa wannan kukan kaman yanka ki zaayi?..." Cikin kuka tace
"Nidai banso..." Ayan murtuke fuska yayi yaje wajen drawer da ya ajiye drugs dinta ya dauko ya fara mixing Maganin, yana hadawa kukan ihsan da kara volume, yanmatan mikewa sukayi banda husna, tsayawa yayi kanta
"Stand up..." Ya umarceta, daga kanta tayi ta harareshi tana hawaye,
"Pls kiyi sauri ya tafi kalan baici abinci ba yazo don taimaka...." Husna bata idaba ya katseta dacewa
"Tashi mana!..." Ya fada cikin fada, ahankali ta mike tana kokarin mika mashi hannun ta, girgiza kai yayi
"Wannan bana jijiya bane...na bombom ne..." Yafada babu wasa fuskan shi, kallon shi tayi
"Gaskiya Aa...in dai bazaka yimin a hannu ba ka barshi kawai..." Tafada sounding serious, baki ya tabe
"Ok...bari in fadawa dad dinki..after all shi ya kawoni nan..." Ya fada
"Ka bari in kirawo anty Zuwairat...." Husna ta fada
"Wallahi ki bari..." Inji ihsan dake kuka Husna bata saurareta ba ta yi hanyan kofa,da sauri ihsan tace
"Dan Allah ki dawo....zan bari..." Ta fada cikin kuka, Ayan tsaye yayi yana kallon ta haka nan sai yayi tunanin ina ma matarshi ce
"Stop it..." Yafada cikin zuciyanshi, husna dawo dakin tayi ihsan ta rungume husna ta bashi baya still tana sanye da hijab,
"Ke dalla cire hijab dinki ko so kike ni in cire maki...." Ya daka mata tsawa, ahankali ta daga bayan hijab dinta tana kuka, nan ya hango well shaped hips dinta sanye da skirt na less, baisan sanda yayi biting lower lip dinshi ba, dukawa yayi ya dan yi kasa da skirt dinta white skin dinta ya bayyana, ihsan sai kuka take Ahankali ya soka mata injection ta saki ihu sai dariya ta kufce mashi
"Ke wallahi kin fiya son jikinki..."
"Ba wa wani son jiki...zalunta ta kawai kake..." Tafada cikin kuka, husna tureta tayi daga jikinta saboda haushi da kishi.

Atakaice kullum sai yazo yayi mata allura Kuma yace dole sai a bombom, Kuma kullum inyazo sai tayi mashi tsiwa Kuma one thing shine the more yana ganinta the more yana zama attached to her, ko kadan yasan bazata bashi chance ba, amma confirm he has fallen for her amma hakan bai hanashi yi mata injection na mugun ta ba. Bayan kwana 3 da rasuwan Mahmoud mami ta umarci husna data koma gida don zata aiketa Maiduguri, ba haka husna taso ba amma dole ta koma gida.

A week later around 5:30pm ihsan ta rako wata cousin sis dinta datayi visiting dinta, suna cikin tafiya ta hango motan Ayan, da sauri ta kauda kanta gefe don ba karamin kunyan shi take jiba, horn yayi masu amma bata daga kanta ba, murmushi yayi Sannan yace
"My patient where are you going?.." Ya fada da karfi yanda zataji shi daga inda take, banza tayi dashi yakara cewa
"Patient ki koma gida ko anjuma in nazo maki injection inyi maki mai zafi..." Tana kin haka ta daga kanta ta harareshi tacigaba da tafiya shi Kuma ya wuce yana dariya
"Waye wancan?.." Inji cousin dinta,
"Rabu dashi...mugune..." Ta fada mashi, dariya cousin dinta tayi Sannan tace
"Mai white blood da alaman wancan yanason ki..." Da sauri ihsan ta kalleta ta tabe baki
"Allah ya sauwake.. Wancan azzalumi?.."
"Ai is written all over him...Allah dai ya zaba maki Wanda yafi alkhairi..."
"Ameen sis...amma banda wancan..." Dariya cousin dinta tayi tana cewa
"Nidai gani da 5 months pregnancy dina Kuma am so excited... I can't wait kiji yanda mukeji..."

Hiransu suka cigaba dayi har sis dinta ta hau adaidaita ta tafi gidanta.

Bayan sallan magrub yaje gidansu don bata injection sai kuka take as usual ta dafe bango tare da bashi bayanta, duk bombom dinta yayi ja saboda yanda yake tsira mata allura for the past one week, ja yayi gaskiya he can't bear hearing her cry for his wickedness anymore, juyar daita yayi tare da ajiye injection dake hannun shi,
"Yanzu let's negotiate..." Ya fada mata ahankali, Dan hararanshi tayi Sannan tace
"Wane irin negotiation?..." Ta tambayeshi tana goge hawayenta,
"Na farko kar ki kara hararata... Na biyu zan baki number ta ki kirani...if you don't zan zo gobe for more injection... Accepted?.." Ya tambayeta, shuru tayi for a moment Sannan tace
"Ni gaskiya bazan kirakaba....." Bata idaba yace
"Ok...bani ass dinki...." Da sauri tace
"Zan kiraka..." Murmushi yayi
"Dats good... Yanzu kawo phone dinki..." Ya umarceta,
"Ban fito dashiba..." Ta fada mashi kasancewan yanzu a dakin baki yake yi mata injection,
"Kije ki dauko mana...." Ba musu ta fita ta dauko wayanta tana ta tunanin manufan shi
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: 💙💜❤🖤💛💚
KAWARTA CE SANADI
❤💛💚🖤💙💜


®zuwairat( ummu Maryam)8⃣

*Fans ina godiya da sonku agareni Kuma ina baku hakuri kan yanda bana samun reply messages dinku especially my Facebook fan, Allah ya barni tare daku, you guys are really awesome, I heart you all, thanks* 💋♥


Ayan kallon Abba yayi Sannan yayi saurin dauke kanshi, dukda haushin ihsan yakeji at that moment sai da ya tausaya mata. Dad kam sauri kawai yake Ayan da handsome da biye dashi.

Har sanda suka shiga falon ihsan bata tashi ba, babu irin jijjigan da baayi mataba amma shuru, da ka shigo falon sai kayi tunanin ta mutu don banda kuka babu abinda ke tashi ba kaman husna Wanda kukanta ya bambamta dana kowa don abinda ke ranta daban Dana sauran, da gudu dad yashigo handsome na biye dashi, da sauri ya amshe ta daga hannun anty ya fara girgiza ta yana
",momina...mommy pls don do this to me...." Sallama
Ayan yayi ya shiga falon, da sauri husna ta daga kanta ta kalleshi, shima da sauri ya karaso ya durkusa gaban dad dake zaune kasan carpet kan ihsan kan kafanshi, hannun ta ya rike don jin vita sign nan ya samu palse,
"Pls someone should get me a cup of water..." Bai idaba husna ta mike da gudu ta dauko cup cike da ruwa ta mika mashi in the process hannun su ya hadu which husna tayi intensionally, Ayan kam bai maida hankalikanta ba so bai San abinda tayi ba, ruwa ya diba cikin tafin hannun shi ya watsa mata a fuska, ajiyan zuciya ta sauke,da sauri Ayan ya koma baya ya tsaya, ahankali ta bude idanuwanta, dad ta gani,da sauri tace
"Dad...Ku bani wayata in kira yaya Mahmoud...." Nan su Janna da mom suka kara fashewa da kuka, kallon su tayi daya bayan daya amma Allah bai bata daman ganin Ayan dake tsaye gefe ba.
"Dad why are they crying?...nasan karya suke lafiyan Mahmoud lau...kawai mom Ku bani wayata in kirashi Ku gani...." Tafada fuskan ta babu hawaye ko dai su Janna kam sai share hawaye take, wayan dad ne ya fara vibrating da sauri ihsan tace
" dad waye?.." Dad duba wayan yayi yaga uncle din Mahmoud, picking dad yayi uncle Mahmoud ya sanar dashi abinda ke faruwa
"Eh an sanar da mu..." Inji dad,
"Da gaske ne ya rasu?.." Ihsan ta tambayi dad,
"Momina kiyi hakuri...." Girgiza kanta tayi tafara murza kafafunta kasa tana kuka tare dacewa
"Wayyo yaya Mahmud ka dawo..." Tafada cikin kuka mai ratsa zuciyan mai saurare, Ayan tsaya kallon ikon Allah yayi
"If you love him so much why don't you follow him..." Yafada cikin zuciyanshi.
Kuka ta dingayi tana dirje kafafunta akasa
"Ke dalla rufewa mutane baki...an fada maki kuka akeyiwa mamaci?...." Anty ta daka mata tsawa, da sauri ta kama bakinta amma kirjinta sai up and down yake saboda yanda take kukan zuciya,
"Kaina...wayyo kaina ne ke yimin ciwo...." Tafada cikin matsanacin kuka, dad daga kai yayi ya kalli Ayan alaman pls help, husna kam kuka take amma duk hankalin ta yana kan Ayan shi Kuma baisan Allah ya ajiyeta wajenba, sai kallon gashin kan ihsan yake kasancewan kanta babu dankwali, sai kallon yanda kirjinta ke tashi yake kawai sai ya tsinci kanshi da jin haushin kukanta, husna kam sai kukan bakin ciki da haushi take
Ahankali ya kara takawa zuwa inda take, daga idanuwa tayi ta ganshi, ita dake kuka sai ta daure fuskanta tare da watsa mashi kallon haushi batasan ya akayi ya zo gidansu ba amma ko ma meye batason shi cikin gidansu, durkusawa yayi zai taba kanta nan take tayi baya da kanta tana cewa
"Dad ni wannan ya tafi a kiramin anty sakinat,..." Bata idaba anty Zuwairat ta daka mata tsawa da
"Kar ki rainawa mutane hankali mana....kai duba and pls give her the necessary help..." Tafada Ayan, cikin jin haushin kallon da tayi mashi yasa yace
"Ku kaita dakinta...zan rubuta injections da drip a sayo sai in sa mata...." Ihsan najin injections ta kwalla ihu
"Wallahi ban so...wannan mugune....wayyo kaina Ku kiramin yaya Mahmud... Wayyo Allah na shiga uku..." Tafada cikin kuka,
"Wai bazaki rufe mana baki ba?..." Anty ta kara daka mata tsawa, shuru tsyi amma bata bar hawaye ba.
"Pls give me a paper and a pen..." Yayi directing maganan shi to Janna Wanda daya ganta yasan kanwar ihsan ce, da sauri husna ta mike itama Janna ta mike tana goge hawayen fuskan ta, school bag dinta ta dauko daga mini library dake gefen falo ta bude ta dauko pen da paper ta mika mashi. Amsa yayi ya rubuta prescription har dana zalunci, don yasan abinda ke damunta will be heal with time,
"Gashi...zaa yi mata injections 2 everyday for 10 days...." Ihun ihsan ya hanashi kara magana don sauran kadan dariya ta kufce mashi
"Wallahi mugune....karya yake...wallahi zaluntata zaiyi...." Afusace mom ta taso ta bige mata baki sai ta kara fashewa da kuka tana kallon Ayan, irin kallon ka tausaya min amma sai ya fakaici idanuwan mutane ya kashe mata ido daya tare da sakin murmushi for just 1 second Sannan ya daure kaman bashi yayi dariya ba
"Kuma zaayi mata Karin ruwa biyu...." Ya karasa maganan shi
"Wallahi ban so...." Tafada cikin tsiwa at the same time tana kuka, dad mikewa yayi zai amshi prescription din
"In babu Wanda zai sayo bari in sayo..." Ayan ya fadawa dad ,
"Ok...bari in dauko maka kudi...." Dad ya fada yana kokarin mikewa,
"Don't worry sir..." Ayan ya fada yana fita daga falon, da sauri husna ta bishi sai da ya fita waje ta ce
"Ka kawo in sayo...ko I should follow you... In case.. Zaa bukaci wani Maganin..." Juyowa yayi ya kalleta sannan ya tabe baki ba tare dayace kala ba ya tafi,
"This girl don't know how very annoying she is...." Ya fadawa kanshi yana fita daga gidan. Gidansu ya koma ya dauki kudi da machine ya fita bayan ya shaidawa Abba da Umma, yana tuki yana dariya
"Daman na sai ranar da kikayi aure zan fidda ran cin ubanki...." Yafadawa kanshi yana dariya sosai.
Dad part dinshi ya koma ya fara shaidawa yan uwa da abokan arziki abinda ke faruwa, anty ta mikar da ihsan suka tafi dakinta tare da husna, itama Janna na biye dasu Anty ta koreta ya mom kam zamatayi nan falo tana kuka.
Husna sai kuka take kaman ita akayiwa mutuwa,
"Ke dalla rufe mana baki muji magana..." Anty ta daka mata tsawa, itama rufe bakinta tayi amma kaman ihsan hawaye basu bar zubowa ba, ihsan sai shessheka take, gani take her world has come to an end cos har yanzu bata yarda Mahmoud is gone ba
"Somebody wake me up...from... This.. Bad dream...ya Allah kasa mafarki nake..." Tafada cikin hawaye,
"Haba daughter... Dukkan mu nan lokaci muje jira...kiyi hakuri... Allah zai kawo maki Wanda yafi alkhairi... Adua kawai zaki dinga yi mashi...kinji habibty..." Anty ta fada mata tana jawota jikinta, fashewa tayi da kuka sosai tana tuna irin hiran da sukayi dashi jiya,
"Anty my heart hurts badly... Ciwo yake min..." Tafada tana dafa kirjinta
"Sorry kinji...bari wannan doc ya dawo..." Sai lokacin ihsan ta tuna dashi, sabon kuka ta fara
"Anty banason shi...."
"Ai ba soyayya akace kiyi dashiba...checking dinki zaiyi kawai..."
"To anty lafiya ta lau ...Dan Allah..."
"Shsssss..." Anty ta fada mata, shuru tayi hawaye yacigaba da kwararowa.

Bayan dad ya gama kiran family da waya ya dawo falo ba Dade ba Ayan yayi sallama ya shigo da ledan kayan da ya sayo.
Dad dake dafe da kanshi ya daga kai ya kalleshi Sannan ya umarci janna data kaishi dakin ihsan, bene ta hau ya bi bayan ta yana Dan Satan kallon yanda gidan take, wani kofa ra bude, ihsan daga kanta tayi daga janna da Ayan aikam sai ta fashe da kuka don ita da allura wara duka don ko kadan batason allura, yana shiga dakin ya ajiye ledan bakin gado ya dauko allura tare da wani roba na daure hannu,
"Your hand..." Ya fada mata, volume ta karawa kukanta tana kankame Anty, hannun ta anty ta mika mashi sai ihu take, hannun ta ya rike kawai sai ya tsinci kanshi da jin wani irin abu da bai tabaji ba, daure hannu ta yayi sosai sai ihu take,
"Kai ka bi ahankali mana...." Anty ta fada mashi, banza yayi daita yacigaba da abinda yake, saida ya daure tamau Sannan ya fara neman jijiya, husna kam tamkar ta hadiye zuciya ta mutu don ko takalmin ihsan batason Ayan ya taba amma ga hannun shi cikin nata,
"Da na Sani da ban raba aurenta da previous suitors din ta ba...da yanzu tana gidan mijinta... Never the less you are mine..." Tafada cikin ranta tana kallon keyan Ayan dake sheki saboda yanayin gyaran gashin kanshi. Cannula ya dauko, runtse idanuwanta tayi tana kuka, tafin hannun ta ya saka cikin nashi Sannan ya tura alluran cikin vein dinta, ihu ta saki sosai kaman an figi maganan daga bakinshi sai cewa yayi
"Sorry..."
"Don't tell me sorry... Kawai ka ciremin wannan abun ..." Tafada cikin tsiwa, baisan lokacin da ya saki wani kasaitaccen murmushi ba, kallon dakin yayi yana Neman inda zai rataya drip, bag hanger ya hango ya cire dukkan bags da sauri husna ta taso tana amsa bags din daga hannun shi bag hanger din ya dauka ya kawo bakin gado yayi fixing drip Sannan ya umarceta ta kwanta, tana hawaye amma fuskan ta daure don Allah kadai yasan irin haushin shi da takeji , drip ya sa mata yayi alluran bacci cikinta. Ko minti ashirin batayiba bacci yayi gaba daita. Yana tsaye gefe yana kallon beautiful face dinta with adoration har tayi bacci, yana kallon ta husna na kallon shi, shi baisan husna tanayi ba itama ihsan batasan yanayi ba,
"Hajiya zan koma gida.. Zuwa anjuma zan dawo in cire mata...." Yafadawa anty
"Daman nan kusa kake ne?.." ta tambayeshi
"Eh..." Ya amsa mata yana ajiye sauran Maganin ta kan bedside drawer.

Fita yayi husna ta bishi,
"Ka tsaya in baka ko ruwane kasha..." Ta fada mashi tana bin bayanshi
"Tofah..." Ya fada yana juyawa don kallon ta,
"Ai you have tried.. You deserve a treat..." Ta fada mashi cikin sanyin murya kanta kasa
" thanks for the treat.. Am OK..." Ya fada yana barin wurin komawa tayi cikin dakin ihsan dake bacci Anty tana rike da hannun ta da aka sawa drip.

Direct masjid ya wuce yayi sallah Sannan ya dawo gida, yau bai tarda antymu falon Umma ba dole yayi serving kanshi yaci abinci amma to his surprise sai yaji he wants to go back and watch the drip drop to the end
[25/11, 22:41] Yar Niger Frd Husaini: ❤💚💛🖤💜💙
KAWARTA CE SANADI
💜💛💚🖤💙❤®zuwairat( ummu Maryam)


1⃣0⃣
Ahankali ta karaso inda yake ya ta mika mashi wayan ya amsa ya saka mata number dinshi tare dacewa
"Yanzu gashi na saka maki...ki kirani by 9:30..." Kallon shi tayi tare da hararanshi as usual
"Oh you forgot what I told you ko?...nace ki bar hararata.." Ya fada cikin Dan bacin rai, Dan turo baki tayi tare dacewa
"Mancewa nayi..."
"Wallahi ki cigaba da mantawa ni Kuma bazan manta dayi maki injection ba..." Yafada knowing shi ne abinda zai iya scaring dinta dashi at all times,
"Now karfe nawa nace ki kirani?..." Ya tambayeta
"9:30.." Ta amsa mashi atakaice Kuma under her breath
"Banji ba..."
"9:30..."
"Good...na tafi..." Batace kala ba tabi bayanshi da harara y fito itama ta fito ta shiga falo. Direct upstairs ta nufa don tunda akayi wannan rasuwan bata zama falo always tana dakinta thinking about how short life is, har yanzu bata bar kuka ba amma ba kaman wancan lokacin ba, wayanta ta dauka tayi dailing number husna.

Husna na ce kwance kasan carpet kanta kafan wata tsohuwar mata wacce daga ganinta kasan an sha duniya, Matan fara ce da akwai wani abu kaman H a gaban goshinta daga ganinta kasan grandma dinta ce, Matan sai shafa kanta take, wayanta ne ya fara ringing ta dauka ta duba, tana ganin ihsan taja wani irin irritating tsoki ta ajiye wayan gefenta, tsohuwar kallon ta tayi
"Bazaki dauki wayan ba?..ko na sariki na ne?.." Ta tambayeta, tsoki husna ta karaja Sannan tace
"Wata yar iska ce Wallahi.. Ai kinsan ni har yanzu bani da saurayi... Duk wayanda ke zuwa are not serious..." Tafada tana sauraron wayanta dake faman ringing,
"Ki kwantar da hankalin ki..dudu shekarunki nawa?..." Husna daga kanta tayi ta kalli Matan
"20 fa...ai na isa aure Wallahi...Kuma yanzu wani nakeso amma Sam baisan da zamana ba..." Inji husna, tsohuwar kallon ta tayi Sannan tace
"Hala shiyasa kika kanjame kamar kudin guzuri?...ki kwantar da hankalin ki...don wannan ba wani abu bane..." Wayanta ne ya fara ringing Kuma ta Kara dubawa taga still ihsan ce, kaman bataso tayi picking
"Kawas ya kike?..." Daga Chan bangaren ihsan dake zaune kan gado ta amsa mata dacewa
"Ina kika ajiye wayanki na kiraki baki daga ba?..."
"Ina bathroom ne..." Tafada tana hararan wayan kaman mutum
"Ok..ya Maiduguri ya grandma?..."
"All is fine..ya injections.. Har yanzu bai bar baki ba?..." Ta tambayeta seeking for information,
"Hmm dats why na kiraki....kinsan abinda ya faru?..." Ihsan ta tambayeta, da sauri husna ta gyara zama tana cewa
"Bani insha kawas ban San abinda ya faruba..." Nan ihsan ta kwace yanda sukayi da Ayan ta fada mata without hiding anything, dafa kirjinta tayi har grandma nacewa lafiya, da sauri ta mike ta bar wurin
"Yanzu kiranshi zakiyi!...." Ta tambayeta muryan ta na rawa kaman zatayi kuka,
"Do I have a choice?..." Kuka husna ta farayi don jitayi she can't control her emotions
"Sis what happened?...." Ihsan ta tambayeta cikin tension,
"Wallahi Mahmoud na tuna...yau ne ya kamata kuyi aure amma Allah bai amince gashi har zakiyi wani saurayin... Har kin mance da Mahmoud...."
Tafada cikin kuka sosai kaman thats the real reason, Da sauri ihsan tace
"Why are saying such?... Waye sabon saurayin...?" Tafada tana shirin kuka
"Wannan Ayan mana..."
Kuka ihsan ta farayi
"Yanzu abinda zakice kenan?... Kinsan ko zan so mutum banda wannan Dan iskan.... You don't know what I have pass through tun ranar da ya fara bani allura cikin visitors room...." Da sauri husna tace
"Wani abu yake yi maki?..." Ta tambayeta cikin tashin hankali
"Ba wani abu yake yimin ba...amma sai yace in cire hijab dina...ya dinga kallon kirjina..." Kuka sosai husna ta dingayi tana cewa
"Anya ba sonki yake?..." Bata idaba ihsan ta katse shi dacewa
"Allah ya sauwake..."
"In kika kirashi yace yanason ki fa?...what will you say?.." Da sauri ihsan tace
"Kam I will spit on him...not after the many holes he have put on my ass..." Dan sanyi husna taji cikin ranta, one thing she knows about ihsan very well is that bata karya, komai na cikin ranta fada mata take Kuma exactly the way it is,
"Ok...Dan Allah ko yace yanason ki karki amince... Mutane zasuyi tunanin bakison Mahmoud..." Dan dariya ihsan tayi tana cewa
"Kodai kina ciki ne....." Bata idaba husna ta katseta dacewa
"Cikin ina?..."
"Cikin Ayan..." Tsoki husna taja tare dacewa
"Amma kin raina min hankali...sam baiyi min ba....he don't have the quality of my ideal man..." Tafada tana shafa heart dinta don tasan confirm no Ayan no life for her,,
"Ok...anyway bari in kashe don yace 9:30 dot zan kirashi kar inyi exusting credit dina..."
"Ok.." Kawai husna tace tana katse wayanta, kwantawa tayi tana karajin Ayan cikin system dinta.

Ayan wanka yayi ya zauna daure da towel as usual ya tisa wayanshi a gaba yana jiran kiran ihsan, bai taba budurwa ba sai lokacin dayake ABU Zaria Kuma suna gamawa school suka mance da juna, amma yanzu he's realizing what true love is tunda gashi ya sa wayanshi gaba yana jiran call din mace, sai haushin kanshi yakeji da bai amshi number ta ba, counting time ya dingayi har lokacin yayi..
Ihsan kam ba don son ranta ba ta yi dailing number dinshi, Ayan na ganin wayanshi ya kawo wuta yayi saurin daukan waya amma baiyi picking ba saida ta kusa tsinkewa Sannan yayi picking tare dacewa
"Hello..who is this?." Yafada kaman baisan wace ba, wani irin gululu ne ya taunuke zuciyan ihsan, batace kala ba ta katse wayanta
Yana ganin an kashe wayan ya saki dariya tare da sake dailing number ta, ringing ya dinga yi ihsan na kallon wayan har ta tsinke bata dauka ba
"Da rabon zakisha injection gobe kenan..." Ya fadawa kanshi yana kara dailing numberta, saida ta kusa tsinke wa Sannan tayi picking Kuma batace komai ba, kaman baisan wace ba yafara cewa
"Babyna na yayi kike..." Yafada cikin sweet voice... " da sauri ihsan ta kalli wayan ta ajiye shi kan gado tare da maidawa hands free, Ayan yacigaba dacewa
"Habibty ko laifin danayi maki dazun da rana Dana zo ne kike fushi har yanzu?... Am sorry... Yanzu who is the owner of this new number?..." Yafada yana murmushi, ihsan tsoki taja tare dacewa
"Malam kace in kira Kuma da kira so sai anjuma..." Da sauri Ayan yace
"Wai kece?...to haka mukayi dake?...ai yanzu ni na kiraki...so yanzu zan kashe wayata sai ki kirani ..in Kuma ba kudi cikin wayanki I understand...." Tsoki ta kara bugawa tana cewa
"Nifa zan kashe wayata tunda na kira...."
"Kika kara yimin tsoki wallahi gobe sai nayi maki injection... Kuma kika kara cewa zaki kashe wayanki kinsan sauran..." Turo baki tayi tana hararan wayan kaman shine zaune gabanta tana son yi tsoki amma bata iyawa,
"To yanzu gani say what you want to say..bacci nakeji..." Dariya Mara sauti yayi
"Ya ajikin ki?..." Ya tambayeta cikin whisper, tabe baki tayi
"Wane jikin?...."
"Jikin ki mana? Wanda kika sha allurai sha hudu saboda shi..." Yafada yana dariyan mugun ta,
"Kai kanka kasan lafiyata lau ka zalunce ni...Kuma Allah sai ya sakamin..."
"Daga taimako sai ki fara tsinemin?...to yanzu a bar wannan maganan...kiyi hakuri in kina jin haushina kan injections din nayi maki...." Bai idaba tace
"Marin dakayimin fah?..."
"To shima kiyi hakuri..." Yayi magana kaman bashi ba, itama ihsan tsaya kallon wayan tayi cos bata taba jin muryan shi kwance haka ba,
"Kinji kiyi hakuri.. Bazan Kara ba..kinji sister...." Shuru dai tayi batace kala ba
"Say something mana...." Ahankali tace
"Na yafe injections din amma Marin sai na rama zan yafe...." Bata idaba dariya ya kufcewa Ayan
"Yanzu ihsan in ma baki fuskata sai ki mareni?....." Ya fada sounding surprised
"Ka bani ka kagani mana...ni da nake mace baka ji nauyin marina ba sai ni zanji nauyin marinka?.... Aa wallahi..." Tafada cikin fada
"Amma kin fiya fada..."
"Kai Kuma ka fiya zalunci..."
"Nidake munyi match kenan..." Baisan sanda maganan ta kufce mashi ba, da sauri ya kama bakin shi yana sauraron reply dinta,ihsan kurawa wayan ido tayi tana tunanin abinda yace amma sai tayi pretending kaman batasan abinda yace ba
"Ni zan kwanta...sai da safe...."
"Nifa na kiraki Kuma sai kice min saida safe?....gaskiya ban yarda ba...bari mu Dan kara hira kadan"
"Ni bacci nakeji..." Tafada atakaice,
"Ni bani jin bacci... Yanzu kin yafemin?...."
"No..."
"Yanzu meye mafuta?..."
"In rama kawai..." Shuru Ayan yayi yana tunanin yanda yake da pride da ego mace ta mareshi? Amma Kuma bakinshi cewa yayi
" yanzu ki fito nima zan fito saiki rama marinki...." Yafada yana mikewa Kuma fuskan shi dauke da murmushi,
"Ka bari sai gobe yanzu bacci zanyi..."
"Aa ki fito yanzu ko Kuma ki yafe...am on my way..." Yafada yana katse wayan. Da sauri ya saka boxer tare da jean ya dauki riga ya saka ya fito rike da wayan.

Yana kashe wayanshi ihsan ta mike zaune daga kan gado tana zaro idanuwa tare da dariya
" he's kidding right?... " ta tambayi kanta,
"Hmmm if he thinks am joking then he's wrong..." Ta fadawa kanta tana dailing number husna.

Daman tun 9:30 da ihsan ta fadawa husna zata kira Ayan taketa trying number ihsan sai taji shi busy, hankalin ta ba karamin tashi yayiba don gani take soyewa kawai suke, kuka ta farayi dataga har kusan ten minutes number ihsan busy
"Ya Allah why is his love killing me?... Is it the punishment for my offence?... Wallahi in har wannan ne sakayyar abinda nayi mata to tayi tsanani..." Tafada tana kuka Kuma hannun ta dafe da chest dinta, kara trying number ta tayi taji still busy ta kara rushewa da sabon kuka, kwantawa tayi tacigaba da trying number ta gaji don kanta ta ajiye wayan, tana ajiyewa ya fara ringing da sauri ta dauki wayan tana ganin ihsan ta gallawa wayan harara tare dacewa tare dacewa
"Banza..." Sannan tayi picking tana cewa
"Babe har na fara bacci.. Ya dai?...." Tafada tana gyara muryan ta don kar ihsan ta gane abinda ke faruwa.
Nan ihsan ta fada mata duk hiran da sukayi dashi
"Wai har dacewa munyi matching saboda yanayin characters dinmu..." Husna sai goge hawaye kawai take amma kukan bai fitowa, ihsan ta cigaba dacewa
"Yanzu yana kan hanya zaizo in rama marina Kuma wallahi ramawa zanyi..." Ta fada tana dariya, husna hararan wayan tayi Sannan ta ce
"Kawai ki fada mashi karyazo...ki yafe mashi...ga Mahmoud is no more.. Duniya is nothing..." Tafada kaman wata aminiyar kwarai.
" to shikenan yaci darajanki...bari in kirashi in fada mashi kar yazo..." Tafada husna bata saurareta ba ta kashe wayanta tana cigaba da kuka.

Ihsan dailing number Ayan tayi yana fara ringing yayi picking tare dacewa
"Ki fito na karaso..." Ya fada muryan shi babu wasa idanuwa ta zaro
"Ka barshi na yafe maka..." Bata idaba ya katseta dacewa
"Ke kar ki raina min wayau...ki fito wallahi gani ina jiranki..." Yafada yana katse wayan shi tare da jingina da gate don daman yana niyyan kiranta ta kirashi.

Ihsan tafi minti biyar zaune bayan ta shaidawa husna abinda yace, ji tayi kaman ta mutu ta katse wayanta kawai with out saying a word.

Mikewa tayi ta dauki praying hijab dinta ta fito lokacin falo ba kowa ta fito gidan wayam saida ta tada maigadi ya bude mata ta leka waje ta ganshi jingine da gate, fuskan shi murtuke yace
"Kifito ki rama..." Yafada babu, bata fitoba ya tace ka barshi kawai na yafe maka... " bata idaba ya fixgota waje
"Ki rama nace..." Idanuwa ta zaro
"I said na yafe..." Tafada cikin tsiwa, tsaya kallon glowing face dinta yayi Sannan ya kama hannun ta ya dora bisa face dinshi
"Ki rama..." Yafada yana kallon eyeball dinta,
Kokarin zare hannun ta tayi amma yaki sakin hannun ta
"Revenge..." Yafada wannan Karin muryan shi bai fitowa sosai don ba karamin effect hannun ta ke dashi kan skin dinshi ba,
"Ihsan my heart is beating ...very fast...and I think it is because of you...." Yafada kaman an fixgi maganan daga bakinshi, da sauri ta zare hannun ta daga cikin nashi dake manne kan fuskan shi ta shige gida da sauri.


❤💜♥💚💙
domin karanta full na wannan littafin danna download da ke kasa


Share this


Author: verified_user

0 Comments: