11 May 2019
Hukuncin wanda ya yi wa budurwa asiri dan ya aureta

HUKUNCIN WANDA YAYI WA YARINYA ASIRI
(SIHIRI) DOMIN YA AURETA :
TAMBAYA TA 2638
*****************
SALAMUN ALAIKUM MALAM,
Dafatan kana lafiya Allah ya saka maka da gidan
aljannah malam bisa fadakar damu da kakeyi
Allah ya biyaka,
Malam ina hukuncin wanda yayiwa iyayen
yarinya da yarinya sihiri ya auri 'yar su bayan
yasan bata sonsa suma dama basa sonci da 'yar
su meye hukuncin sa,
kuma malam shin yin hakan ya halatta?
AMSA
*****
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Shi dai idan an ce sihiri kalmar larabci ce.
Fassararta da harshen hausa kuma, ita ce
"Tsafi". Kuma shi tsafi yinsa haramun ne bisa
Alqur'ani da Sunnah. Duk wanda yayi tsafi to ya
kafirta.
Shi irin wannan nau'in sihirin ana kiransa "Sihrul
Mahabbah". Kuma yana daga cikin mafiya
hatsarin nau'o'in tsafi wadanda yinsu yakan jefa
mutum acikin hallaka.
Mafiya yawa daga cikin Sahabbai da magabata
sun tafi akan cewa duk wanda yayi tsafi
kowanne iri ne ya kafirta. Kuma haddinsa shine
kisa. Sun dogara ne da ayar nan ta 102 a suratul
baqarah tare da hadisi marfu'i wanda Imamut
Tirmidhiy ya ruwaito ta hanyar Jundub Al Azdiy
(ra) yace "HADDIN MATSAFI SHINE A SARE
WUYANSA DA TAKOBI".
Tabaraniy ma ya ruwaitoshi acikin MU'UJAMUL
KABEER Juzu'i na 2 shafi na 1666. Kuma shine
fatawar Imamu Ahmad da Shafi'iy.
Kuma an ruwaito cewa Nana Hafsatu matar
Manzon Allah (saww) wata baiwarta tayi mata
sihiri. Don haka tayi umurni akan kasheta. Haka
kuma Sayyiduna Umar bn Khattab (radhiyallahu
anhu) alokacin halifancinsa ya rubuta zuwa ga
Gwamnoninsa cewa "Ku kashe duk wani matsafi
da matsafiya".
Ta kowacce fuska dai wannan mutumin bai
kyauta ba. Kaja hankalinsa ya tuba zuwa ga
Allah yaje ya warware wannan tsafin da yayi,
kuma ya sabunta imaninsa ya rika dogaro ga
Allah akan dukkan bukatunsa.
WALLAHU A'ALAM

Share this


Author: verified_user

0 Comments: