11 May 2019
Rarraba masarautar kano haramun ne in ji sarkin kano sanusi lamido sanusi

Home Rarraba masarautar kano haramun ne in ji sarkin kano sanusi lamido sanusi
RABA MASARAUTAR KANO, HARAMUN NE.
Farkon abinda ya fara kawo rarrabuwar kawuna a Musulunci shine kekketa masarautu. A zamanin Manzon Allah (SAW) da na Khalifofi kawunan al'ummar Musulmi a hade yake, amma daga sanda aka fara keta Daular Musulunci zuwa gida biyu, har yau kawunan al'ummar Musulmi bai sake haduwa.
Kasashe irinsu Saudia, Iraq. Syria, Bahrain, Dubai, Qatar da kusan dukkanin Kasashen Larabawa da dukkansu Masarauta daya ce, amma daga sanda aka kekketasu zuwa masarautu, har yau basu taba kaunar junansu ba.
Kafin zuwan Ganduje masarautar Kano a dunkule take waje guda, duk da girman Kano da dinbin al'ummar dake cikinta Sarkinmu daya, muna kaunar junanmu, muna san Junanmu, mutanen birni na kaunar na kauye, na kauye na kaunar na birni, babu wanda ke jin haushin wani balle gaba, amma duk wannan na kokarin zama tarihi a yanzu. Domin a yanzu gaba da kiyayya da rarrabuwar kawuna sakamakon kekketa masarautu da ke gwamnatin Kano ke kokarinyi, wannan ko kadan ba zai haifar mana da da mai ido ba.
Kuma Manzon Allah (SAW) ya hanemu da rarrabuwa, kuma yayi Allah wadai da wanda ya raba kawunan al'ummarsa. Dan haka ayi hattara.
pls ku yi sharing zuwa facebook da whatsapp da sauran shafukan sada zumunci mun gode

Share this


Author: verified_user

0 Comments: